Ƙungiyar Tagwaye ta Najeriya ta yi Barazanar Kauracewa Babban Zaɓen Shekarar 2027

Daga Bashir Gasau.   Gidauniyar Tallafawa Tagwaye Maza da Mata ta Najeriya wato Twin Brothers and Sisters Empowerment Foundation, ta yi barazanar kauracewa babban zaben kasar na shekarar 2027.   Mataimakan Shugabannin Kungiyar na Najeriya, Hassan da Hussaini Haruna Koki, ne suka baiyana hakan a yayin babban taronsu na ranar Tagwaye ta Duniya da ya […] The post Ƙungiyar Tagwaye ta Najeriya ta yi Barazanar Kauracewa Babban Zaɓen Shekarar 2027 appeared first on GTR .

Ƙungiyar Tagwaye ta Najeriya ta yi Barazanar Kauracewa Babban Zaɓen Shekarar 2027












Daga Bashir Gasau.

 

Gidauniyar Tallafawa Tagwaye Maza da Mata ta Najeriya wato Twin Brothers and Sisters Empowerment Foundation, ta yi barazanar kauracewa babban zaben kasar na shekarar 2027.

 

Mataimakan Shugabannin Kungiyar na Najeriya, Hassan da Hussaini Haruna Koki, ne suka baiyana hakan a yayin babban taronsu na ranar Tagwaye ta Duniya da ya gudana a jihar Kano a ƙarshen makon da ya gabata.

 

Sau Ɗaya Tinubu Yake Cin Abinci a Kullum Kuma a Wasu Lokutan da Ƙafa Yake Zuwa Ofis – Adedeji

 

A cewar Twin Koki, “Zamu Umarci Dubban Mambobinmu na jihohin Najeriya su Kauracewa Zaɓen shekarar 2027, a sakamakon yadda ake watsi damu Tagwaye a Gwamnatance, duk da yawan da muke dashi a cikin al’umma”.

 

Sun kara da cewa abin takaici ne yadda mahukuntan suke sanya dukkan wasu bangarori na al’umma a cikin aiyukansu na yau da kullum, amma kuma su yi watsi da Tagwaye ba tare da duba yawansu da kuma girman baiwar da Ubangiji ya yi musu ba.

 

A karshe sun ce matuƙar gwamnatin tarayya da na Jihohi ba su waiwaye su ba domin su ji bukatunsu kuma su taimaka musu, toh kuwa babu wasu Tagwaye da za su kaɗa ƙuri’a a zaben shekarar Baɗi.

 

Masarautar Kano ta Musanta Labarin Sarki Sunusi ya Samu Carry Over a Jami’ar Northwest

The post Ƙungiyar Tagwaye ta Najeriya ta yi Barazanar Kauracewa Babban Zaɓen Shekarar 2027 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow