Najeriya da Jamus Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zuba Jarin Dala Milyan 428

Daga Bashir Gasau.   Gwamnatocin ƙasashen Najeriya da Jamus sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar haɗin guiwa, ta bunƙasa tattalin arziki da zuba jari na milyoyin daloli, da nufin ciyar da muhimman sassa gaba a fadin kasar.   ​Yarjejeniyar, wadda ta kai ta dalar Amurka milyan 428, an kulla ta ne a birnin tarayya Abuja, […] The post Najeriya da Jamus Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zuba Jarin Dala Milyan 428 appeared first on GTR .

Najeriya da Jamus Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zuba Jarin Dala Milyan 428

Daga Bashir Gasau.

 

Gwamnatocin ƙasashen Najeriya da Jamus sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar haɗin guiwa, ta bunƙasa tattalin arziki da zuba jari na milyoyin daloli, da nufin ciyar da muhimman sassa gaba a fadin kasar.

 

​Yarjejeniyar, wadda ta kai ta dalar Amurka milyan 428, an kulla ta ne a birnin tarayya Abuja, inda ta mayar da hankali kan tallafawa fannonin makamashi, aikin gona, kiwon lafiya, da bunkasa dabarun dogaro da kai, baya ga inganta kamfanoni masu zaman kansu domin samar da aiyukan yi.

 

An ga Watan Babbar Sallah (Zulhijja) a Ƙasar Saudiyya

 

​Muhimman abubuwan da Yarjejeniyar ta Ƙunsa sune:

 

1. ​Makamashi da Lantarki: Karfafa sauye-sauyen da ake yi a ɓangaren wutar lantarki a Najeriya

 

2. ​Aikin Gona da Kiwon Lafiya: Kyautata harkar abinci da samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya

 

3. ​Masana’antu: Tallafawa tsare-tsaren Najeriya na fadada masana’antu da kasuwanci.

 

A ƙarshe Jami’an gwamnatin Jamus sun baiyana yarjejeniya a matsayin wani babban mataki da zai tabbatar da zuba jari na dogon lokaci, tare da ƙarfafa dankon zumuncin kasuwanci tsakaninsu da Najeriya, wadda ita ce kasa mafi ƙarfin tattalin arziki a fadin Nahiyar Afirka.

 

Turakin Dawakin Misau ya Rasu a Yayin da Yaje Ƙasar Saudiyya Domin Aikin Hajji

 

The post Najeriya da Jamus Sun Ƙulla Yarjejeniyar Zuba Jarin Dala Milyan 428 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow