‘Yan Sandan Kano da Al’ummar Gari Sun Kama Gungun Wadanda Ake Zargi Sun Ƙware Wajen Fashin Adaidaita Sahun Mutane

Daga Bashir Gasau.   Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano tare da haɗin guiwar al’ummar gari, sun sami nasarar kama wasu gungun mutane da suka Ƙware wajen fashin Adaidaita Sahu bayan sun zuba wa matukansa abin gusar da hankali.   Kakakin rundunar na jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan ta cikin […] The post ‘Yan Sandan Kano da Al’ummar Gari Sun Kama Gungun Wadanda Ake Zargi Sun Ƙware Wajen Fashin Adaidaita Sahun Mutane appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Kano da Al’ummar Gari Sun Kama Gungun Wadanda Ake Zargi Sun Ƙware Wajen Fashin Adaidaita Sahun Mutane












Daga Bashir Gasau.

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano tare da haɗin guiwar al’ummar gari, sun sami nasarar kama wasu gungun mutane da suka Ƙware wajen fashin Adaidaita Sahu bayan sun zuba wa matukansa abin gusar da hankali.

 

Kakakin rundunar na jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce tuni wasu masu tuka Adaidaita Sahu guda goma da aka taba yi wa irin wannan fashi a unguwannin Dorayi da Bachirawa sun bayyana tare da gano wadanda aka kama a matsayin mutanen da sukai musu.

 

Kotu ta Yanke wa Mutanen da ta Samu da Laifi a Sace Ɗaliban Jihar Oyo Hukuncin Ɗaurin Rai da Rai

 

A cewar Kiyawa, “Da misalin karfe 11:30 na daren ranar Talatar da ta gabata ne muka sami kiran gaggawa a Ofishin ‘Yan Sanda na Dala kan cewa wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun yaudari wani matashi mai suna Abdulrahman Atula, wanda ke sana’ar tuka Adaidaita Sahu inda suka ba shi abun sa maye, sannan suka yi masa fashi da makami tare da ƙwace masa babur ɗinsa mai ƙafa uku.

 

An Bankaɗo Yadda Gwamnatin Najeriya ta Ware Naira Bilyan 30 don Gyaran Gidajen Sarakuna da Wuraren Ibada

 

Bayan samun rahoton aka tura tawagar sintiri zuwa wurin da taimakon sahihan bayanan sirri da hadin kan al’umma, jami’an suka gudanar da bincike mai zurfi wanda ya kai ga kama Usman Ashiru da Abubakar Ali, mazauna unguwar Rijiyar Lemo, da ake zargi da fashi da makami tare da kwato babur ɗin da aka sace a hannunsu.

 

Adan haka Rundunar ta yi kira ga duk wani mai Adaidaita Sahu da aka taba yi wa irin wannan fashi a cikin Birnin Kano da ya gaggauta zuwa Ofishin ‘Yan Sanda na Dala ko ya tuntubi Baturen ‘Yan Sandan Ofis Din (DPO) ta lambar waya 08036885094 domin shigar da ƙorafi.

 

Rashin Tsaron Najeriya Zai Zama Tarihi Nan ba da Jimawa ba – Akpabio

The post ‘Yan Sandan Kano da Al’ummar Gari Sun Kama Gungun Wadanda Ake Zargi Sun Ƙware Wajen Fashin Adaidaita Sahun Mutane appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow