Rasuwar Kaftin Umar Bakori me Ritaya Babban Rashi ne ga Tsaron Najeriya – Shugaban Ƙungiyar Sintiri na Jihar Neja

Daga Bashir Gasau.   Shugaban Ƙungiyar Sintiri na Jihar Neja, Nasir Mohammed Manta, ya baiyana rasuwar shugabansu na Najeriya, Navy Captain A.B Umar Bakori me ritaya, a matsayin babban Rashi ga harkokin tsaron ƙasar nan.   Nasir Manta, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa, a lokacin da ya ke baiyana alhininsa […] The post Rasuwar Kaftin Umar Bakori me Ritaya Babban Rashi ne ga Tsaron Najeriya – Shugaban Ƙungiyar Sintiri na Jihar Neja appeared first on GTR .

Rasuwar Kaftin Umar Bakori me Ritaya Babban Rashi ne ga Tsaron Najeriya – Shugaban Ƙungiyar Sintiri na Jihar Neja












Daga Bashir Gasau.

 

Shugaban Ƙungiyar Sintiri na Jihar Neja, Nasir Mohammed Manta, ya baiyana rasuwar shugabansu na Najeriya, Navy Captain A.B Umar Bakori me ritaya, a matsayin babban Rashi ga harkokin tsaron ƙasar nan.

 

Nasir Manta, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa, a lokacin da ya ke baiyana alhininsa bisa rasuwar shugaban kungiyar na Kasa, wanda Allah ya yiwa rasuwa a daren jiya, Talata.

 

Rahoton Taron Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya da JIBWIS ke Jagoranta a Najeriya

 

A cewar Manta, “Ba zan manta da darrusan da na koya daga marigayin ba, adan haka ina addu’ar Ubangiji ya gafarta masa kuma ina mika sakon ta’aziyya ta ga iyalai, yan uwa da kafatanin mambobin kungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya a bisa wannan babban rashi da muka yi”.

 

Za dai a gudanar da Jana’izarsa da misalin karfe 1 na ranar Yau Laraba, a gidansa da ke Kinkinau ta jihar Kaduna.

 

Yau Ranar Matasa ta Duniya (International Youth Day)

The post Rasuwar Kaftin Umar Bakori me Ritaya Babban Rashi ne ga Tsaron Najeriya – Shugaban Ƙungiyar Sintiri na Jihar Neja appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow