Majalisar Amurka ta Buƙaci a Daina Tallafawa Najeriya Har Sai an Daina Kashe Kiristoci

Daga Bushira Aminu, Kano.   Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dokokin Amurka ya gabatar da wani ƙudirin doka da ya gindaya wasu sharuɗɗan dakatar da tallafin kuɗi ga Najeriya har sai gwamnatin ƙasar ta magance matsalar hare-hare a sassan kasar.   Ƙudirin ya mayar da hankali ne kan tallafin da Amurka ke bayarwa don tsaron […] The post Majalisar Amurka ta Buƙaci a Daina Tallafawa Najeriya Har Sai an Daina Kashe Kiristoci appeared first on GTR .

Majalisar Amurka ta Buƙaci a Daina Tallafawa Najeriya Har Sai an Daina Kashe Kiristoci

Daga Bushira Aminu, Kano.

 

Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dokokin Amurka ya gabatar da wani ƙudirin doka da ya gindaya wasu sharuɗɗan dakatar da tallafin kuɗi ga Najeriya har sai gwamnatin ƙasar ta magance matsalar hare-hare a sassan kasar.

 

Ƙudirin ya mayar da hankali ne kan tallafin da Amurka ke bayarwa don tsaron ƙasa, da shirye-shirye masu alaƙa na kasafin kuɗin shekarar da zai ƙare a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2027.

 

Tinubu ya Naɗa, Joseph Tegbe, a Matsayin Ministan Lantarki

 

Da yake magana a kan ƙudirin a shafinsa na X, ɗan majalisa Riley Moore ya ce: “Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ta kashe miliyoyi wajen roƙon majalisar, amma ta kasa magance matsalar kashe kiristoci a ƙasar”.

 

Moore ya ƙara da cewa ba za su rufe idanunsu suna kallo “ana yi wa ƴan’uwansu kiristoci kisan ƙare dangi ba.”

 

Babban Lauyan Gwamnatin Najeriya ya Buƙaci a Rushe Wasu Jam’iyyu Ciki Har da ADC

 

Ƙudirin da aka gabatar ya tanadi cewa aƙalla kashi 15 na dala biliyan 6.89 da aka ware, za su tafi ne wajen taimaka wa tsaro a Afirka, inda aka ware dala milyan 870 domin yaƙi da ta’addanci.

 

FFS Gombe ta Horas da Jami’anta Kan Dabarun Ceto Waɗanda Iftila’i ya Shafa

 

A ƙudirin da aka gabatar, ya bayyana cewa ba za a iya fitar da kashi 50 na kudaden da aka ware wa Najeriya ba har sai sakataren harkokin wajen ƙasar ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya “ta ɗauki ƙwararan matakai na hana tashe-tashen hankula da kuma daukar matakin hukunta masu laifi”.

 

Sai dai ba a bayyana ainihin kuɗaden da aka ware wa Najeriya a cikin ƙudirin dokar ba.

 

BBC Hausa.

 

Gwamnatin Najeriya ta Aiyana Jibi Jumu’a a Matsayin Ranar Hutun Ma’aikata

The post Majalisar Amurka ta Buƙaci a Daina Tallafawa Najeriya Har Sai an Daina Kashe Kiristoci appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow