Ma’aikatar Ilimin Najeriya ta Gudanar da Rangadi a Wasu Jihohin Arewa Maso yamma Kan Ilimin Almajirai

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ofishin mai taimakawa Ministan ilimin Najeriya Kan karatun Almajirai, tsangayu da Makarantun Allo, Dakta Balarabe shehu Kakale Shuni, ya gudanar da wani rangadi a jihohin Arewa Maso yammacin kasar.   Kakale ya gudanar da Rangadin ne a jihohin Kaduna da Kano da kuma Jigawa, da nufin karawa juna ilimi kan […] The post Ma’aikatar Ilimin Najeriya ta Gudanar da Rangadi a Wasu Jihohin Arewa Maso yamma Kan Ilimin Almajirai appeared first on GTR .

Ma’aikatar Ilimin Najeriya ta Gudanar da Rangadi a Wasu Jihohin Arewa Maso yamma Kan Ilimin Almajirai

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ofishin mai taimakawa Ministan ilimin Najeriya Kan karatun Almajirai, tsangayu da Makarantun Allo, Dakta Balarabe shehu Kakale Shuni, ya gudanar da wani rangadi a jihohin Arewa Maso yammacin kasar.

 

Kakale ya gudanar da Rangadin ne a jihohin Kaduna da Kano da kuma Jigawa, da nufin karawa juna ilimi kan manufofin gwamnatin tarayyar na tabbatar da tsarin nan na Bai-daya kan inganta ilimin tsangayu da Makarantun Allo da kuma Yadda za a aiwatar da Shi Wato “National Policy on Almajiri Education and Implementation guidelines”.

 

INEC ta Sauya Ranar Zaɓen da ya Fado a Watan Ramadan na Shekarar Baɗi

 

A cewarsa, “Manufar rangadin na mako guda a wasu daga cikin jihohin Arewa Maso yammacin Najeriya shine, tabbatar da tsarin bai-daya na ingantawa da gyarawa da kuma yadda za a aiwatar da ilimin tsangayu da Makarantun Allo a jihohin Najeriya”.

 

A yayin ziyarar, sun tattauna da Masu ruwa da tsaki kamar Kwamishinonin ilimi da Manyan Sakatarorin a ma’aikatar da Shugabanin majalisun dokokin jihohi da na Kwamitin ilimi, domin ganin an zamanantar da fannin ilimin tsangayu da Makarantun Allo dama Rayuwar Almajirai kamar Yadda tuni ma’aikatar ilimin Najeriya bisa jagorancin, Dakta Tunji Alausa da Farfesa Suwaiba Ahmed suka himmata.

 

Karin Hasken Shugaban PCACC Kano Kan Kwato Motocin da Tsaffin Kwamshinoni Suka Tafi Dasu

 

Hadimin Ministan ilimin ya kuma ce za su ci-gaba da tuntuba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin kai wa ga cikakkiyar nasara.

 

A ƙarshe ya jaddada cewa wannan na daya cikin ƙudirin gwamnatin Najeriya na sabunta fata (Renew Hope Agenda), dake da Manufar ganin kowanne dan kasa ya sharbi romon Demokradiyya kamar yadda Shugaba Tinubu ya tsara.

 

Zamu Zaƙulo Dukkan Mutanen da Suka Rasa Wani Sashe na Jikinsu Domin Kula Dasu a Fadin Najeriya – HAF’D

The post Ma’aikatar Ilimin Najeriya ta Gudanar da Rangadi a Wasu Jihohin Arewa Maso yamma Kan Ilimin Almajirai appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow