Koyi da Gwamnatin Kogi Wajen Yaki da Ta’addanci Zai Haifar da Kyakkyawan Sakamako a Najeriya – Ardon Masauratar Kogi ta Yamma

 Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ardon masauratar Kogi ta yamma dake karamar hukumar Yagba ta jihar Kogi, Alhaji Babuga Mai Rali, ya bukaci gwamnatin jihohin da suke fama da matsalar tsaro, da suyi koyi da gwamnatin jiharsu ta fuskar aiki da Kungiyoyin Sa-kai.   Babuga ya baiyana hakan ne a yayin da yake tofa albarkacin […] The post Koyi da Gwamnatin Kogi Wajen Yaki da Ta’addanci Zai Haifar da Kyakkyawan Sakamako a Najeriya – Ardon Masauratar Kogi ta Yamma appeared first on GTR .

Koyi da Gwamnatin Kogi Wajen Yaki da Ta’addanci Zai Haifar da Kyakkyawan Sakamako a Najeriya – Ardon Masauratar Kogi ta Yamma












 Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ardon masauratar Kogi ta yamma dake karamar hukumar Yagba ta jihar Kogi, Alhaji Babuga Mai Rali, ya bukaci gwamnatin jihohin da suke fama da matsalar tsaro, da suyi koyi da gwamnatin jiharsu ta fuskar aiki da Kungiyoyin Sa-kai.

 

Babuga ya baiyana hakan ne a yayin da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da nasarar ceto mutum huɗu da aka sace, a yayin harin da ƴan bindiga suka kai wata makaranta dake ƙaramar hukumar Dekina.

 

Gwamnatin Yobe za ta Kashe Naira Milyan 460.8 Wajen Tallafawa Masu Tuyar Kosai dai Sauran Kananan Sana’o’i

 

A cewarsa, “Nasarar da Gwamnatin Kogi da jami’an tsaron jihar ke samu ta kasance babban abin yabo a sakamakon aiki da Kungiyoyin Sa-kai da Gwamna Usman Ododo ke yi”.

 

Mafari kenan da ya bukaci sauran jihohin dake makwabtaka da jihar ta Kogi, musamman jihohin Ekiti da Kwara da su baiwa Kungiyoyin Sa kai hadin kai da nufin kaiwa ga cikakkiyar nasara.

 

Haka kuma ya yabawa gwamna Ododo, a bisa goyon bayan da gwamnatinsa ke baiwa Kungiyoyin Sa-kai da masu rike da Sarautun gargajiya wajen kokarin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasar.

 

Cikakken Rahoton Yadda Kaza ta Kwana a “Cell”, Saboda yi wa Manomi Ta’adi a Gonarsa Dake Kano

 

Haka zalika, shugaban al’ummar Fulani Makiyaya ya godewa mashawarcin gwamna kan harkokin tsaro, Kwamanda Omodoro Duru Jeri Mai ritaya, a bisa yadda suke aiki da su ka’in da na’in.

 

A ranar talatar da ta gabata ne aka sace dalibai tare da shugaban makarantar da kuma wani ma’aikacin wucin gadi na hukumar shirya jarrabawar NECO, a yayin harin da mahara suka kai makarantar da ke Odo-Ekina.

 

Addu’a Kadai ba Zata yi Maganin Matsalolin Najeriya ba, Sai an Daina Abubuwa 5 – Abdulkarimu Daiyabu

The post Koyi da Gwamnatin Kogi Wajen Yaki da Ta’addanci Zai Haifar da Kyakkyawan Sakamako a Najeriya – Ardon Masauratar Kogi ta Yamma appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow