Jami’ar FUDMA ta Dakatar da Ɗalibai 20 Bisa Zarginsu da Satar Jarrabawa

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) dake jihar Katsina, ta amince da hukuncin dakatar da ɗalibai 20 bisa samun su da laifukan satar Jarrabawa da kuma fara aiwatar da dokar halartar aji ta kashi 75%.   Daraktan Sashen yada labarai da Hulda da Jama’a na jami’ar, Nasiru M. Abdul, ne […] The post Jami’ar FUDMA ta Dakatar da Ɗalibai 20 Bisa Zarginsu da Satar Jarrabawa appeared first on GTR .

Jami’ar FUDMA ta Dakatar da Ɗalibai 20 Bisa Zarginsu da Satar Jarrabawa

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) dake jihar Katsina, ta amince da hukuncin dakatar da ɗalibai 20 bisa samun su da laifukan satar Jarrabawa da kuma fara aiwatar da dokar halartar aji ta kashi 75%.

 

Daraktan Sashen yada labarai da Hulda da Jama’a na jami’ar, Nasiru M. Abdul, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, inda ya ce dakatarwar za ta fara aiki daga zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2025/2026.

 

Azabtar da ‘Yan Adawa ba Zai Hana Kada Jam’iyyar APC Daga Sama Har Ƙasa ba – Na Hannun Daman El-Rufa’i

 

A cewar Nasiru, “An amince da hukuncin ne bayan Majalisar gudanarwar jami’ar ta karɓi rahoton Kwamitin Ladabtar da Dalibai, a yayin taronta na 138 da aka gudanar ranar Laraba, 11 ga watan Maris na Shekarar 2026, wanda ya gudana a dakin taro na Twin-Theatre da ke Harabar jami’ar”.

 

Da yake jawabi, Shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammed Khalid Othman, ya baiyana cewa an ɗauki matakin ne bisa tanadin sashe na 13, sakin layi na 3(c) na dokokin jami’ar da suka shafi magudin Jarrabawa da kuma rashin da’a a harkokin karatu.

 

Ina Aka Kwana a Aikin Man Kolmani Bayan Shekaru Uku – Tambayar Sanata Matori ga Tinubu

 

Farfesa Othman ya kuma yabawa mambobin kwamitin a bisa jajircewarsu wajen bin dokokin jami’ar, inda ya ce an bawa dukkan daliban da abin ya shafa damar kare kansu a gaban kwamitin kafin a yanke hukunci, don tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bin ka’idojin da suka dace a binciken.

 

A ƙarshe ya ce hukuncin na nufin aikawa da sako mai karfi ga dukkan dalibai don su guji aikata satar Jarrabawa, domon ya zama darasi ga duk wanda yake da aniyar karya dokokin jami’ar.

 

Ma’aikatar Ilimin Najeriya ta Gudanar da Rangadi a Wasu Jihohin Arewa Maso yamma Kan Ilimin Almajirai

The post Jami’ar FUDMA ta Dakatar da Ɗalibai 20 Bisa Zarginsu da Satar Jarrabawa appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow