Gwamnatin Kano ta Sanar da Lokacin Hutun Ƙarshen Zango Karatu na Biyu na Shekarar 2025/2026

Daga Bashir Gasau.   Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da ranar fara hutun ƙarshen zangon karatu na biyu na shekara ta 2025/2026.   Daraktan Wayar da Kai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar, Musbahu Aminu Yakasai, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda […] The post Gwamnatin Kano ta Sanar da Lokacin Hutun Ƙarshen Zango Karatu na Biyu na Shekarar 2025/2026 appeared first on GTR .

Gwamnatin Kano ta Sanar da Lokacin Hutun Ƙarshen Zango Karatu na Biyu na Shekarar 2025/2026

Daga Bashir Gasau.

 

Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da ranar fara hutun ƙarshen zangon karatu na biyu na shekara ta 2025/2026.

 

Daraktan Wayar da Kai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar, Musbahu Aminu Yakasai, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce dukkan makarantun Furamare da Sakandire na je ka ka dawo mallakar gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar, za su tafi hutun a gobe Juma’a 17 ga watan Afrilu, a inda Makarantun kwana za su tafi hutun a Jibi Asabar 18 ga Afrilun shekarar 2026.

 

Durƙushewar Tattalin Arziƙi da Rushewar Masana’antu na Barazana ga Haƙƙin ‘Yan Najeriya – ICHR

 

A cewar Yakasai, “Hutun zai bai wa dalibai da ma’aikata damar hutu da kuma shiri kafin fara zangon karatu na uku, wanda ake sa ran Makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi 3 ga watan Mayu, a inda makarantun je ka ka dawo, za su koma a ranar Litinin 4 ga watan Mayun shekarar 2026, domin fara ɗaukar karatun sabon zangon”.

 

Zantawar Aljanun Bogi da Rundunar ‘Yan Sandan Kano Kan Yadda Suke Damfarar Mutane

 

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Gwani Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yiwa ɗalibai fatan alheri a lokacin hutun, inda ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su tabbatar ‘ya’yansu sun koma makaranta akan lokaci domin kauce wa tangardar karatu, harma ya bukaci shugabannin makarantu da su bi tsarin kalandar karatun da aka amince da ita ba tare da sabawa ba.

 

A ƙarshe Makoda ya jaddada kudirin Gwamnatin Kano na tabbatar da samar da ingantaccen yanayin koyo da kuma kiyaye kyawawan ka’idoji a bangaren ilimi.

 

Daga Zaɓen 2027 na Daina Fitowa Takara – Atiku Abubakar

The post Gwamnatin Kano ta Sanar da Lokacin Hutun Ƙarshen Zango Karatu na Biyu na Shekarar 2025/2026 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow