Budaddiyar Wasika ga Al’ummar Jihar Kano – Ambasada Mukhtar Gashash

    Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.   Yaku al’ummar Jihar Kano Masu daraja,   Da farko ina miƙa godiyata ga Allah Maɗaukakin Sarki tare da nuna cikakken kishina da nauyin da ke kaina ga jiharmu mai albarka. Ina rubuta wannan wasiƙa ne domin sanar da ku a hukumance cewa na yanke shawarar tsayawa […] The post Budaddiyar Wasika ga Al’ummar Jihar Kano – Ambasada Mukhtar Gashash appeared first on GTR .

Budaddiyar Wasika ga Al’ummar Jihar Kano – Ambasada Mukhtar Gashash

 

 

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.

 

Yaku al’ummar Jihar Kano Masu daraja,

 

Da farko ina miƙa godiyata ga Allah Maɗaukakin Sarki tare da nuna cikakken kishina da nauyin da ke kaina ga jiharmu mai albarka. Ina rubuta wannan wasiƙa ne domin sanar da ku a hukumance cewa na yanke shawarar tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar Accord Party.

 

Wannan shawara ba ta zo cikin gaggawa ba. Ta biyo bayan shawarwari da tuntuba mai zurfi da masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma, matasa, mata, ƙwararru da sauran ’yan kishin Kano waɗanda ke da burin ganin jiharmu ta samu ci gaba mai ɗorewa.

 

Jam’iyyar ADC Tsagin Nafiu Bala ta Tabbatar da Chris Uba a Matsayin Dan Takararta na Shugaban Kasa

 

Jihar Kano jiha ce mai tarihi, al’adu masu daraja, dimbin albarkatun ɗan Adam da kuma damar ci gaba mara iyaka. Duk da haka, har yanzu muna fuskantar ƙalubale a fannoni da dama kamar ilimi, lafiya, tsaro, samar da ayyukan yi ga matasa, bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.

 

Na fito neman wannan kujera ne saboda na yi imanin cewa Kano na buƙatar shugabanci wanda zai fifita muradun jama’a fiye da muradun kai. Muna buƙatar gwamnati mai gaskiya, riƙon amana, adalci da kuma wadda za ta samar da ci gaba ga kowa ba tare da nuna bambanci na siyasa, ƙabila ko addini ba.

 

‘Yan Fashin da Ake Zargin Sun Addabi Kasuwar Daji Sun Shiga Hannun ‘Yan Sandan Zamfara

 

Hakazalika, ina da ƙudurin kawo sauyi a tsarin siyasar Kano. Siyasa bai kamata ta kasance ta cin mutunci, zagi, tada hankali ko rarrabuwar kawuna ba. Ya kamata siyasa ta kasance ta hidima, gaskiya, mutunta juna da kuma gabatar da manufofi masu anfani ga jama’a. Lokaci ya yi da za mu yi watsi da gurɓatacciyar siyasa tare da rungumar siyasa mai tsafta da mutunci.

 

Manufofina ga Jihar Kano sun haɗa da:

 

• Inganta ilimi ga yaranmu.

• Ƙarfafa tattalin arzikin matasa da mata.

• Samar da ingantattun ayyukan lafiya.

• Gina da inganta ababen more rayuwa.

• Bunƙasa noma da tabbatar da wadatar abinci.

• Kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

• Yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kawo ƙarshen daba da rashin tarbiyya a cikin al’umma.

• Tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan shugabanci.

 

Chief Nwanyanwu ya Zama Dan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar ZLP

 

Ina roƙon goyon bayanku, addu’o’inku da shawarwarinku yayin da za mu fara wannan tafiya tare. Wannan gwagwarmaya ba ta mutum ɗaya ba ce, gwagwarmaya ce domin gina Kano mafi alheri ga wannan zamani da kuma al’ummomin da za su zo nan gaba.

 

Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya shiryar da mu, Ya albarkaci Jihar Kano, Ya ba mu hikima da ƙarfin gina makomar da al’ummarmu ta cancanta.

 

Nagode ƙwarai da gaske, kuma Allah Ya albarkaci Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.

 

Naku mai biyayya,

Amb. Dr. Mukhtar Gashash

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano (2027)

Jam’iyyar Accord Party

 

Amfani da Sashe na Biyu na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Zai Magance Matsalar Tsaron Ƙasar – Tsohon Mataimakin Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya

The post Budaddiyar Wasika ga Al’ummar Jihar Kano – Ambasada Mukhtar Gashash appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow