Ba Ma Iya Barci da Ido Biyu – Mazaunin Dukku Kan Barazanar ’Yan Ta’adda

Daga Bashir Gasau.   Wani mazaunin ƙauyen Malala na karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe, Alhaji Musa Gurya, ya baiyana cewa rayuwarsa na cikin hatsari a sakamakon yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai musu farmaki gidansu harma suka hallaka Kaninsa, inda shi kuma Allah ya kubutar da shi.   APC ta yi Tunani me Kyau […] The post Ba Ma Iya Barci da Ido Biyu – Mazaunin Dukku Kan Barazanar ’Yan Ta’adda appeared first on GTR .

Ba Ma Iya Barci da Ido Biyu – Mazaunin Dukku Kan Barazanar ’Yan Ta’adda












Daga Bashir Gasau.

 

Wani mazaunin ƙauyen Malala na karamar hukumar Dukku ta jihar Gombe, Alhaji Musa Gurya, ya baiyana cewa rayuwarsa na cikin hatsari a sakamakon yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai musu farmaki gidansu harma suka hallaka Kaninsa, inda shi kuma Allah ya kubutar da shi.

 

APC ta yi Tunani me Kyau Wajen Bawa Yari Mukamin Darakta Janar na Yakin Neman Zaɓen Tinubu – Kwamared Baura Lawal

 

A cewar Musa Gurya, “A lokacin da ‘yan ta’addan suka zo sun dauke wayoyin salularmu guda 4 da sabon babur dina, kuma a daren na kira Baturen ‘Yan Sandan Dukku (DPO), don sanar da shi halin da muke ciki kuma shi da kansa ya zo a ka dauki gawar kanina zuwa Malala inda muka yi masa Jana’iza”.

 

Musa ya kara da cewa bayan wata daya da faruwar Iftila’in, barayin sun sake kiran sa suna masa barazana ko ya basu Naira Milyan 5 ko su hallaka shi. Kuma bayan ya kai rahoto wajen DPO na Dukku an bi wayar barayin inda aka kama daya daga cikinsu mai suna Dauda harma aka kai shi CID.

 

Cire Sunan Danjuma Garkuwa a Zaɓen Fidda Gwanin Jam’iyyar ADC Rashin Adalci ne ga Al’ummar Gombe/Kwami/Funakaye – Musa Gebi

 

“Gaskiya ni da sauran ‘yan uwana muna cikin tashin hankali domin bama iya barci da ido biyu, a sakamakon yadda rana tsaka aka saki Dauda ba tare da zuwa kotu ba, duk da na kashe kimanin Naira milyan 5 akan lamarin”.

 

Akan wannan batu mun yi kokarin Jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, DSP Buhari Abdullahi, inda ya baiyana cewa suna gudanar da bincike kuma za su waiwaye mu idan sun kammala.

 

Hotunan Shugabannin Sabuwar Hukumar Bogi ta Najeriya Masu Kula da Aiyukan Jihohi da Wakilan China da Amurka

The post Ba Ma Iya Barci da Ido Biyu – Mazaunin Dukku Kan Barazanar ’Yan Ta’adda appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow