Ƙungiyar Kautal Pulaaku Fulbe ta Bukaci Gwamnatin Bauchi ta Gaggauta Share Gonakin da Suka Toshe Hanyoyin Kiwon Dabbobi

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya (Kautal Pulaaku Fulbe), ta yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi da ta gaggauta ɗaukar matakan share Gonakin da suka toshe hanyoyin gefen titi da ke da tazarar (Miter 45) a ɓangarorin biyu.   Shugaban kungiyar na Najeriya, Dakta Hussein Muhammed Buzayu, ne yayi wannan kira […] The post Ƙungiyar Kautal Pulaaku Fulbe ta Bukaci Gwamnatin Bauchi ta Gaggauta Share Gonakin da Suka Toshe Hanyoyin Kiwon Dabbobi appeared first on GTR .

Ƙungiyar Kautal Pulaaku Fulbe ta Bukaci Gwamnatin Bauchi ta Gaggauta Share Gonakin da Suka Toshe Hanyoyin Kiwon Dabbobi












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya (Kautal Pulaaku Fulbe), ta yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi da ta gaggauta ɗaukar matakan share Gonakin da suka toshe hanyoyin gefen titi da ke da tazarar (Miter 45) a ɓangarorin biyu.

 

Shugaban kungiyar na Najeriya, Dakta Hussein Muhammed Buzayu, ne yayi wannan kira a yayin zantawarsa da GTR Hausa a Abuja, inda ya ce kiran ya biyo bayan sabuwar dokar Burtali da gwamnatin jihar Bauchi ta sanya.

 

Kungiyar MACBAN ta Bukaci a Gudanar da Cikakken Bincike Kan Harin da Bata-gari Suka Kai Kauyen Otukpo-Nobi na jihar Benue

 

A cewar Buzayu, “Wannan mataki na da matuƙar muhimmanci domin bai wa makiyaya damar yin amfani da haƙƙinsu na doka wajen kiwon dabbobi da zirga-zirga cikin walwala, ba tare da fuskantar wata matsala ba”.

 

Ya kara da cewa bin ka’idar da doka ta samar zai bada damar dorewar zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar, adan ya yi fatan gwamnati da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki za su duba wannan lamari tun kafin ya haifar da wata matsala ta tabarbarewar tsaro.

 

Kotun Daukaka Kara ta Hana INEC Amincewa da Shugabancin Jam’iyyar ADC na Tsagin David Mark

 

Jagororin Kungiyoyin Makiyaya da Manoma a Najeriya kan kara tashi tsaye wajen fadakar da mambobinsu tasirin zaman lafiya, musamman a duk lokacin yanayin damina domin gujewa samun tsamin dangantaka a tsakanin bangarorin guda biyu dake kasancewa tamkar Danjuma da Danjummai.

 

Sarkin Musulmi ya Umarci Al’ummar Najeriya su Duba Jinjirin Watan Safar na Shekarar 1448

The post Ƙungiyar Kautal Pulaaku Fulbe ta Bukaci Gwamnatin Bauchi ta Gaggauta Share Gonakin da Suka Toshe Hanyoyin Kiwon Dabbobi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow