Zamu Taimakawa Shugabannin Siyasa Wajen Aiwatar da Aiyukan da Al’ummarsu ke Buƙata – Farfesa Abdullahi Ya’u

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Hukumar Kwararru ta masu kula da hannun jari da kudi ta Najeriya, ta baiyana mafi yawancin ‘Yan Siyasar ƙasar a matsayin waɗanda suke aiyukan da ba shi al’ummarsu ke bukata ba.   Shugaban Hukumar na Najeriya, Farfesa Abdullahi Ya’u, ne ya baiyana hakan a yayin taron karawa juna sani na […] The post Zamu Taimakawa Shugabannin Siyasa Wajen Aiwatar da Aiyukan da Al’ummarsu ke Buƙata – Farfesa Abdullahi Ya’u appeared first on GTR .

Zamu Taimakawa Shugabannin Siyasa Wajen Aiwatar da Aiyukan da Al’ummarsu ke Buƙata – Farfesa Abdullahi Ya’u

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Hukumar Kwararru ta masu kula da hannun jari da kudi ta Najeriya, ta baiyana mafi yawancin ‘Yan Siyasar ƙasar a matsayin waɗanda suke aiyukan da ba shi al’ummarsu ke bukata ba.

 

Shugaban Hukumar na Najeriya, Farfesa Abdullahi Ya’u, ne ya baiyana hakan a yayin taron karawa juna sani na shekara-shekara kan tsare-tsaren Kuɗi, Nazari da dorewar tattalin Arziki, inda ya ce hakan na faruwa ne a sakamakon rashin tuntuba daga wakilan nasu.

 

Jirage 57 Sun yi Jigilar Maniyyatan Najeriya 23,439 Zuwa Kasar Saudiyya

 

Adan haka ya ce taron na bana ya maida hankali wajen samar da sabon tsarin bin diddigi, na kasafin kuɗin da gwamnati ke bawa ‘Yan Siyasa domin su yi aiki a ƙananan hukumomin Najeriya guda 774.

 

Zamu Taimakawa Shugabannin Siyasa Wajen Aiwatar da Aiyukan da Al'ummarsu ke Buƙata - Farfesa Abdullahi Ya'u

 

A cewar Farfesa Ya’u, “Kafin taronmu na bana mun gudanar da cikakken bincike a dukkan ƙananan hukumomin kasar nan, domin zakulo matsalolin da ke damunsu la’akari da mafi yawancin matsalolin nasu ya bambanta, harma mun samar da wani kundi me taken “Abinda ‘yan kasa suka fi damuwa ayi musu”.

 

An Shawarci Gwamnatin Nijar ta Maida Jihohin Ƙasar 19

 

Bugu da kari ya ce manufar yin hakan shine domin haskawa waɗanda lamuran suka shafa, ta yadda za su magance wa mutanensu matsalolin da ke damunsu domin a ajiye komai a muhallinsa.

 

Zamu Taimakawa Shugabannin Siyasa Wajen Aiwatar da Aiyukan da Al'ummarsu ke Buƙata - Farfesa Abdullahi Ya'u

 

Dadin dadawa ya ce amfani da wannan kundi zai taka muhimmiyar rawa wajen magance manyan matsalolin Najeriya, kamar tsaro, Yunwa, rashin aikin yi da kuma saukakawa ‘yan Siyasa wajen sanin abinda za su yi wa al’ummarsu.

 

Yarjejeniyar Aiki Tsakanin NDLEA da Gidauniyar GMBNI ta Tabbata

 

Taken taron na bana shine, “Da’a wajen kashe Kuɗaɗe, Ci Gaban Kowa da Kowa da Samar da Dorewar Arziki a nahiyar Afirka.

 

Taron na bana ya gudana ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya sami halartar Masana harkokin kudi daga sassa daban daban na Najeriya.

 

Rikici ya Barke a Tsakanin Gwamnonin APC Saboda Batan Kuɗin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu

The post Zamu Taimakawa Shugabannin Siyasa Wajen Aiwatar da Aiyukan da Al’ummarsu ke Buƙata – Farfesa Abdullahi Ya’u appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow