‘Yan Sandan Zone One Sun Kama Wanda Ake Zargi da Guduwa da Wayoyin Ɗaliban Jami’ar Bayero Guda 38

Daga Bashir Gasau.   Rundunar ƴan sandan Najeriya me kula da shiyya ta ɗaya (Zone One) dake Kano, ta kama wani mutum, Richard Peter, bisa zarginsa da guduwa da Wayoyin Ɗaliban Jami’ar Bayero har guda 38.   Kakakin rundunar na Zone One, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da […] The post ‘Yan Sandan Zone One Sun Kama Wanda Ake Zargi da Guduwa da Wayoyin Ɗaliban Jami’ar Bayero Guda 38 appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Zone One Sun Kama Wanda Ake Zargi da Guduwa da Wayoyin Ɗaliban Jami’ar Bayero Guda 38

Daga Bashir Gasau.

 

Rundunar ƴan sandan Najeriya me kula da shiyya ta ɗaya (Zone One) dake Kano, ta kama wani mutum, Richard Peter, bisa zarginsa da guduwa da Wayoyin Ɗaliban Jami’ar Bayero har guda 38.

 

Kakakin rundunar na Zone One, DSP Abdullahi Hussaini, ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce ɗalibai 38 ne suka kai ƙorafin Richard me shekaru 32 ɗan asalin jihar Legas, bisa zargin damfararsu da sunan samar musu aiki.

 

Jam’iyyar APC ta Amince da ‘Yan Takarar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 28 Cikin 114

 

A cewar sanarwar, “Wanda ake zargin ya gayyace su wani Hotal a Sabon Gari ta hannun wata mata mai suna Faith Dauda, inda ya umarce su da su ajiye wayoyi da kayayyakinsu, yana me cewa idan basu yi hakan ba, ba za a yarda da su a wajen aikin ba.

 

Daga nan sai yaje ya siya musu abinci, inda ya shammace su ya koma ɗakin ya kwashe wayoyin da sauran kayayyakin su sannan ya tsere a lokacin da suke tsaka da cin abincin.

 

Kotu ta Mallakawa Sonidep Gidajen Man Kamfanin Star Oil da ke Jamhuriyar Nijar

 

Binciken ƴan sanda ya gano ɗaya daga cikin wayoyin a tashar Kano Line, lamarin da ya taimaka wajen cafke shi a Zariyan jihar Kaduna kafin ya tsere zuwa Legas, sannan an kuma ƙwato wayoyin salula guda 29 da sauran kayayyakin da ake zargin ya sata.

 

A ƙarshe rundunar ta ce tana ci-gaba da bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu, inda ta gargaɗi jama’a da su guji amincewa da tayin aikin da basu tabbatar da sahihancinsa ba.

 

Na Fito Takarar Majalisar Jiha ne Domin Yakar Ɗabi’ar Hausawa na Hana Mata Hakkinsu – Honarabul Aisha ABCD

The post ‘Yan Sandan Zone One Sun Kama Wanda Ake Zargi da Guduwa da Wayoyin Ɗaliban Jami’ar Bayero Guda 38 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow