‘Yan Sandan Gombe Sun Kama Wadanda Suke Zargi da Fashi da Makami, Tare da Kwato Motar Sata da Mukullan Buɗe Gidaje

Daga Aliyu Gerengi Gombe.   Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta sami nasarar kama wasu da take zargi da aikata fashi da makami, tare da ƙwato motar Sata da mukullayen bude Kadarorin al’umma (Master Keys).   Kakakin rundunar na jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya […] The post ‘Yan Sandan Gombe Sun Kama Wadanda Suke Zargi da Fashi da Makami, Tare da Kwato Motar Sata da Mukullan Buɗe Gidaje appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Gombe Sun Kama Wadanda Suke Zargi da Fashi da Makami, Tare da Kwato Motar Sata da Mukullan Buɗe Gidaje












Daga Aliyu Gerengi Gombe.

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta sami nasarar kama wasu da take zargi da aikata fashi da makami, tare da ƙwato motar Sata da mukullayen bude Kadarorin al’umma (Master Keys).

 

Kakakin rundunar na jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa a yau Laraba, inda ya ce sun sami nasarar ne a wasu sumame daban-daban da suka gudanar cikin sa’o’i 24.

 

Akpabio ya Bude Makon Budaddiyar Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ya Buƙaci Kara Gaskiya da Riƙon Amana

 

A cewar sanarwar, “Jami’anmu sun kama wani mai suna Micah Nuhu, a bisa zargin aikata fashi da makami da kuma jikkata wata mata mai suna Mama Kingsley Joseph, bayan ya yi mata rauni da Tabarya sannan ya ƙwace jakarta”.

 

Daga bisani jami’an sun kwato jakar da aka sace, yayin da aka garzaya da wadda aka kai wa harin zuwa Asibitin Cottage da ke Bambam domin samun kulawar likitoci, inda ake ci gaba da neman wani da ake zargin abokin aikinsa ne mai suna Mubarak, wanda ya tsere.

 

Jam’iyyu Uku Sun Makara Yayin da INEC ta Rufe Karbar Sunayen ‘Yan Takara

 

A wani samame na daban kuma, jami’an sun kama Nasiru Aminu mai shekaru 40 da Jamiu Muhammad mai shekaru 33 a wata maboya da ke yankin Tumfure ta Ƙaramar Hukumar Akko, tare da kwato Mukullaye guda 39 (Master keys) da kuma Sukundireba (screwdriver), waɗanda ake zargin suna amfani dasu wajen fasa gidaje.

 

Har ila yau, rundunar ta kwato mota kirar Toyota Yaris da ake zargin an sace bayan wasu bata gari sun kai wa mai motar, Sani Ahmed, hari ta hanyar daba masa wuƙa, tare da jefar da shi daga cikin motarsa a mahaɗar Tumu-Kashere, kafin daga bisani su yasar da motar a kusa da Barikin Sojoji.

 

Majalisar Dokokin Kano ta Soke Dokar da ta Kafa Hukumar KNUPDA

The post ‘Yan Sandan Gombe Sun Kama Wadanda Suke Zargi da Fashi da Makami, Tare da Kwato Motar Sata da Mukullan Buɗe Gidaje appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow