‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Gungun Mutanen da Suka Addabi Al’umma da Fashi da Makami da Damfarar Internet

Daga Aliyu Gerengi Gombe.   Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙi da aikata manyan laifuka, inda ta kama wata ƙungiyar mutane takwas da ake zargi da aikata fashi da makami da damfarar intanet, tare da ceto wani yaro mai shekara takwas da aka sace da kuma kama mutum […] The post ‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Gungun Mutanen da Suka Addabi Al’umma da Fashi da Makami da Damfarar Internet appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Gungun Mutanen da Suka Addabi Al’umma da Fashi da Makami da Damfarar Internet

Daga Aliyu Gerengi Gombe.

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙi da aikata manyan laifuka, inda ta kama wata ƙungiyar mutane takwas da ake zargi da aikata fashi da makami da damfarar intanet, tare da ceto wani yaro mai shekara takwas da aka sace da kuma kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin.

 

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Gombe, inda ya yi bayani kan nasarorin da rundunar ta samu da kuma matakan tsaro da take ɗauka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

A cewarsa, “Bincike ya fara ne bayan wasu mazauna unguwar Wuro Birji da ke ƙaramar hukumar Akko sun kai rahoton cewa wasu mahara sun tare su tare da kwace wayoyin salularsu a ranar 7 ga Yunin 2026”.

 

Rahoton Ziyarar Ta’aziyyar da Sarkin Baburawan Kano ya Kaiwa Dallatun Masarautar

 

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun yi amfani da bayanan da ke cikin wayoyin wajen shiga asusun ajiyar kuɗin waɗanda abin ya shafa ba tare da izini ba, inda suka cire Naira dubu 296 da 790, sannan suka karɓi rancen gaggawa na Naira dubu 205 da 205 ta hanyar yanar gizo.

 

https://www.facebook.com/share/v/1CtpTSw4fz/

 

Kwamishinan ya ce bayanan sirri da binciken fasaha sun kai ga cafke jagoran ƙungiyar, Mustapha Kabiru, wanda aka fi sani da “Musty Bobo”, ɗalibi mai shekara 19 a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kaltungo. Furucinsa ya kai ga kama sauran mutum bakwai da ake zargi suna cikin ƙungiyar.

 

Ya ƙara da cewa bincike ya nuna ƙungiyar na da alaƙa da fiye da hare-hare goma sha uku da suka faru a Wuro Birji, Riyal, Bomala da Jauro Jatau, yayin da ake ci gaba da neman sauran waɗanda suka tsere.

 

Wajibin Dan Najeriya ne ya Fito ya Kawar da Mulkin Zalunci na Jam’iyyar APC – Honarabul Philip Anthony

 

Dangane da aiwatar da dokokin hanya, CP Chuso ya ce rundunar ta tsaurara matakan kama motocin da ke amfani da lambobin rajista da aka rufe, aka lalata, aka sauya ko kuma ba su da lambobin rajista.

 

Ya bayyana cewa tun bayan fara wannan sintiri a ranar 16 ga Yunin 2026, rundunar ta kama motoci 121, yayin da aka gurfanar da mutum 114 a kotu bisa laifin karya dokokin zirga-zirgar ababen hawa.

 

Kwamishinan ya kuma buƙaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa sun yi wa motocinsu rajista tare da sanya lambobin rajista yadda doka ta tanada.

 

Shugaba Tinubu ya Umarci ICPC ta Binciki Hukumar Bogi ta PFIPC

 

Haka kuma, CP Chuso ya sanar da nasarar ceto wani yaro mai shekara takwas da aka sace bayan ya fita daga gidansu a ƙaramar hukumar Akko a ranar 27 ga Yunin 2026.

 

Ya ce binciken da aka gudanar ya kai ga kama Abdullahi Mohammed a Kumo, wanda furucinsa ya taimaka wajen kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a lamarin, wato Mohammed Magaji, Sale Sale da Walida Ya’u.

 

An ceto yaron cikin ƙoshin lafiya tare da miƙa shi ga iyalansa, yayin da ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu.

 

A wani ɓangare kuma, Kwamishinan ya ce rundunar ta ƙaddamar da shirin Yaƙi da Ƙungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Ɗabi’u (POCACOV) domin wayar da kan matasa da ɗalibai game da illolin daba, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka.

 

Hotuna: Yadda CP Omolori ya Ziyarci Garin Azare Kan Rikicin da ya Faru a Tsakanin Kungiyoyin Matasa

 

Ya kuma ce wani samame da aka kai maboyar masu aikata laifuka a cikin birnin Gombe a ranar 7 ga Yuli ya kai ga kama mutum 44, inda aka samu wasu daga cikinsu da makamai masu haɗari, tabar wiwi da sauran miyagun ƙwayoyi.

 

CP Umar Ahmed Chuso ya jaddada kudirin rundunar na ci gaba da gudanar da aikin ‘yan sanda bisa bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma, tare da kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Gombe.

 

An Kuma Hukunta Wasu Alkalai da Ma’aikatan Kotunan Jihar Kano Saboda Aikata Laifuka Daban-daban

The post ‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Gungun Mutanen da Suka Addabi Al’umma da Fashi da Makami da Damfarar Internet appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow