‘Yan Sandan Bauchi Sun Ceto Yaran da Aka Sato Daga Jihar Taraba Aka Boye a Jihar

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta ceto wasu yara mata biyu masu shekaru 13 da aka yi garkuwa da su daga Jihar Taraba tare da kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a aikata laifin haɗa baki da kuma sace yaran a Ƙaramar Hukumar Kirfi.   Kakakin rundunar […] The post ‘Yan Sandan Bauchi Sun Ceto Yaran da Aka Sato Daga Jihar Taraba Aka Boye a Jihar appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Bauchi Sun Ceto Yaran da Aka Sato Daga Jihar Taraba Aka Boye a Jihar

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta ceto wasu yara mata biyu masu shekaru 13 da aka yi garkuwa da su daga Jihar Taraba tare da kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a aikata laifin haɗa baki da kuma sace yaran a Ƙaramar Hukumar Kirfi.

 

Kakakin rundunar na jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an sami nasarar ceto yaran ne bayan wani mutum mai shekaru 57, mazaunin ƙauyen Fangari da ke Ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba, ya kai ƙorafi ga jami’an tsaro a ranar 10 ga Maris din shekarar 2026.

 

Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara

 

Mahaifin yaran ya bayyana cewa diyarsa mai suna Aisha da kawarta Zainab, sun bar gida ba tare da sanin inda suka nufa ba, kuma duk ƙoƙarin gano su bai yi nasara ba.

 

Sanarwar ta ce bayan gudanar da bincike da tattara bayanan sirri, jami’ansu sun gano yaran a garin Bara da ke Ƙaramar Hukumar Kirfi a Jihar ta Bauchi, inda binciken ya nuna cewa wasu matasa biyu, Auwal Muhammad da Abdulgaffar Musa, masu shekaru 20, mazauna Unguwar Zangoma da ke Bara, sun haɗa baki tare da ɗauko yaran daga ƙauyensu ba tare da izinin iyayensu ba.

 

Zazzafan Martanin Jam’iyyar ADC Kan Abubuwan da Suka Faru a Zaben Jihar Ekiti

 

A karshe Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in sace yara ko cin zarafinsu ba, harma ya buƙaci iyaye da masu kula da yara su kasance masu sanya ido sosai a kan yaransu tare da kai rahoton duk wani abu da suka gani na shakku ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

 

Gwamnatin Kano ta Rufe Makarantun Koyar da Aikin Lafiya Guda Biyu

The post ‘Yan Sandan Bauchi Sun Ceto Yaran da Aka Sato Daga Jihar Taraba Aka Boye a Jihar appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow