Ya Kama Gwamnatin Tarayya da na Jihohi Su Hada Karin Albashi da Matakan Saukaka Tsadar Rayuwa – Jabir Bichi

Daga Bashir Gasau.   Matashin Dan Gwagwarmayar nan a Najeriya, Kwamared Jabir A. Bichi, ya shawarci Gwamnatin tarayya da na Jihohi kan Su hada karin albashi da matakan saukaka tsadar rayuwa.   Jabir Bichi, ya bada shawarar ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce karin albashi ba tare […] The post Ya Kama Gwamnatin Tarayya da na Jihohi Su Hada Karin Albashi da Matakan Saukaka Tsadar Rayuwa – Jabir Bichi appeared first on GTR .

Ya Kama Gwamnatin Tarayya da na Jihohi Su Hada Karin Albashi da Matakan Saukaka Tsadar Rayuwa – Jabir Bichi












Daga Bashir Gasau.

 

Matashin Dan Gwagwarmayar nan a Najeriya, Kwamared Jabir A. Bichi, ya shawarci Gwamnatin tarayya da na Jihohi kan Su hada karin albashi da matakan saukaka tsadar rayuwa.

 

Jabir Bichi, ya bada shawarar ne ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce karin albashi ba tare da ɗaukar matakan dakile tashin farashin kayan masarufi ba, zai haddasa tashin farashin kayayyaki da aiyukan yau da kullum.

 

Tinubu Mai Tausayi ne Don Baya Son Ganin Talaka a Cikin Kunci – Abdulaziz Abdulaziz

 

A cewarsa, “Idan gwamnati za ta ƙara wa ma’aikata albashi, toh ya kamata ta sanya ido sosai tare da ɗaukar matakan da za su hana kamfanoni, ‘yan kasuwa da masu samar da kayayyaki yin ƙarin farashi ba tare da hujja ba, domin hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa ma’aikata da talakawa sun amfana da karin albashin a zahiri”.

 

Al’ummar Unguwanni Goma Dake Jihar Bauchi Sun Koka Kan Yadda Kamfanin Lantarki na JED ke Gasa Musu Aya a Hannu

 

Ya kara da cewa akwai buƙatar gwamnati ta samar da ingantattun tsare-tsaren tallafi ga ma’aikata, musamman ta fuskar sauƙaƙa rayuwa a tsakiyar wata, domin rage musu matsin tattalin arziki da tsadar rayuwar da suke fuskanta, wanda ta hakan ne zai ƙara inganta walwalarsu, ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, da kuma rage wahalhalun da talakawa ke ciki.

 

A karshe ya ce rage wani kaso na Harajin da Gwamnatocin tarayya da na Jihohi ke karba a hannun kamfanoni, zai dakile tashin kayan masarufi a Najeriya ko da anyi ƙarin albashin.

 

Gwamnatina za ta Kara Hada Kai da Shugabannin Addinai Domin Inganta Zaman Lafiya da Hakuri da Juna – Tinubu

The post Ya Kama Gwamnatin Tarayya da na Jihohi Su Hada Karin Albashi da Matakan Saukaka Tsadar Rayuwa – Jabir Bichi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow