WOFAN ta Cancanci Yabo ta Fuskar Bunkasa Aiyukan Kafafen Yada Labarai da Ci-gaban Al’umma – Kwamared Jabir Bichi

Daga Amina Rabi’u Gwangwazo.   Dan Gwagwarmayar nan a Najeriya, Kwamared Jabir A. Bichi, ya baiyana kungiyar Mata Manoma ta Najeriya (WOFAN), karkashin jagorancin Hajiya Dakta Salamatu Garba (Garkuwar Aujara), a matsayin wadda ta cancanci yabo ta fuskar bunƙasa aiyukan kafafen yaɗa labarai da ci-gaban al’umma.   Bichi ya bayyana hakan ne ta cikin sakon […] The post WOFAN ta Cancanci Yabo ta Fuskar Bunkasa Aiyukan Kafafen Yada Labarai da Ci-gaban Al’umma – Kwamared Jabir Bichi appeared first on GTR .

WOFAN ta Cancanci Yabo ta Fuskar Bunkasa Aiyukan Kafafen Yada Labarai da Ci-gaban Al’umma – Kwamared Jabir Bichi

Daga Amina Rabi’u Gwangwazo.

 

Dan Gwagwarmayar nan a Najeriya, Kwamared Jabir A. Bichi, ya baiyana kungiyar Mata Manoma ta Najeriya (WOFAN), karkashin jagorancin Hajiya Dakta Salamatu Garba (Garkuwar Aujara), a matsayin wadda ta cancanci yabo ta fuskar bunƙasa aiyukan kafafen yaɗa labarai da ci-gaban al’umma.

 

Bichi ya bayyana hakan ne ta cikin sakon taya murna ga kafar yaɗa labaran GTR Hausa, a bisa kyautar Sabuwar Motar da Kungiyar WOFAN ta basu domin kara inganta aikinsu.

 

Rahoton Yadda WOFAN ta Bawa GTR Hausa da SolaceBase Tallafin Motoci Domin Ƙara Inganta Aiyukansu

 

A cewar Bichi, “Muna yaba wa kokarin Shugabar WOFAN ta kasa da kasa, Hajiya Dakta Salamatu Garba (Ambasadar Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya), na bayar da tallafi domin bunkasa aiyukan kafafen yada labarai da kungiyoyi harma da ɗai-ɗaikun mutane”.

 

Haka kuma ya taya shugabannin kafar da ɗaukacin ma’aikatanta murnar samun wannan tallafi, inda ya ce wannan wani babban ci-gaba ne da zai taimaka wajen kara inganta aiyukan yada labarai, bincike, da kawo wa al’umma sahihan bayanai cikin gaggawa da inganci.

 

Gwamnan Yobe ya Nada Yarima Ibn Mahmud, a Matsayin Sabon Sarkin Ngazargamu

 

Bugu da kari ya baiyana tallafin a matsayin wata alama ta amincewa da irin gudunmawar da kafar ke bayarwa, wajen wayar da kan jama’a da kuma kawo labarai masu amfani ga al’umma, adan haka ya yi fatan bada Motar zai kara karfafa musu guiwa wajen gudanar da aiyukansu cikin kwarewa, gaskiya da kuma rikon amana.

 

A karshe ya yi addu’ar Allah ya saka wa Ƙungiyar WOFAN da Alheri, ya kuma sanya wannan mota ta zama sanadin ci-gaba da samun karin nasarori ga GTR Hausa a aiyukansu na yau da kullum.

 

Hotuna: Gwamnan Sokoto ya Nada Mambobin Hukumar Gudanarwar Manyan Makarantun Jihar

The post WOFAN ta Cancanci Yabo ta Fuskar Bunkasa Aiyukan Kafafen Yada Labarai da Ci-gaban Al’umma – Kwamared Jabir Bichi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow