Wasu Bata-gari Sun Sarewa Sallaman Sarkin Bakar Sarkin Rano Hannu a Kano

Daga Bashir Gasau.   Wasu Bata-gari sun farwa Sallaman Sarkin bakar Sarkin Rano, Malam Bala Isah, inda suka sare masa hannunsa na Dama.   Sakataren Yada Labaran Masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, ne ya tabbatar wa da GTR Hausa hakan ta cikin wata sanarwa inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 […] The post Wasu Bata-gari Sun Sarewa Sallaman Sarkin Bakar Sarkin Rano Hannu a Kano appeared first on GTR .

Wasu Bata-gari Sun Sarewa Sallaman Sarkin Bakar Sarkin Rano Hannu a Kano

Daga Bashir Gasau.

 

Wasu Bata-gari sun farwa Sallaman Sarkin bakar Sarkin Rano, Malam Bala Isah, inda suka sare masa hannunsa na Dama.

 

Sakataren Yada Labaran Masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, ne ya tabbatar wa da GTR Hausa hakan ta cikin wata sanarwa inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:30 na daren ranar 28 ga watan Maris din da ya gabata, a Kanyar Funkuyi da ke Ƙaramar hukumar Bunkure.

 

Ana Zanga-zangar Adawa da Matakin INEC Kan Jam’iyyar ADC

 

A cewar Faragai, “Tunda farko Sallaman Sarkin Bakar ya kaiwa wani mutum, Sauwanu Hadi, ɗauki a lokacin da mutanen ke kokarin kwace masa Babur da kuma wayarsa ta Salula, wanda kuma bayan sun harbe shi da bindiga bata tashi ba, sai suka fara saransa har kuma suka guntule masa hannu”.

 

Amurka da Iran Sun Tsagaita Wuta Kan Yakin da Suke Gwabzawa a Yankin Gabas ta Tsakiya 08=04=2026

 

Da yake karbar rahoton faruwar lamarin, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya bawa Sallaman tallafin Naira Dubu Dari (100,000) domin ya ci-gaba da kula da lafiyar sa, kafin daga bisani ya umarci a gabatar da takardar a gaban baturen ‘yan sandan yankin domin ci-gaba da bincike.

 

A ƙarshe Sarkin ya gargaɗi Hakimai da Dagatai da masu unguwanni harma da sauran jami’an tsaron dake yankin masarautar, da su Ƙara dagewa wajen sanya ido tare da daukar duk Wani matakin da ya dace, kan duk wata bakuwar fuskar da ba’a amince da ita ba domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

 

Majalisar Dokokin Kano ta Janye Tuhume-tuhume Kan Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Gwarzo

The post Wasu Bata-gari Sun Sarewa Sallaman Sarkin Bakar Sarkin Rano Hannu a Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow