Tsohon Grand Khadi na Bauchi ya Buƙaci Gwamnati ta Bawa Mawallafa Littattafai Goyon Baya

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Tsohon Grand Khadi na jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Yakubu Marafa, ya shawarci mahukuntan bangaren Ilimi na Najeriya da su himmatu wajen siyen littattafai da mawallafa ke rubutawa don rabawa a makarantu saboda a bayar da karfin guiwa ga marubutan, don su ci-gaba da wannan aiki.   Abdullahi Marafa ya baiyana […] The post Tsohon Grand Khadi na Bauchi ya Buƙaci Gwamnati ta Bawa Mawallafa Littattafai Goyon Baya appeared first on GTR .

Tsohon Grand Khadi na Bauchi ya Buƙaci Gwamnati ta Bawa Mawallafa Littattafai Goyon Baya

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Tsohon Grand Khadi na jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Yakubu Marafa, ya shawarci mahukuntan bangaren Ilimi na Najeriya da su himmatu wajen siyen littattafai da mawallafa ke rubutawa don rabawa a makarantu saboda a bayar da karfin guiwa ga marubutan, don su ci-gaba da wannan aiki.

 

Abdullahi Marafa ya baiyana hakan ne ta cikin jawabinsa a wajen kaddamar da littattafai guda Uku da Malam Jibrin Mohammed Dan azumi, ya wallafa, inda ya ce idan mutane sun yi kwazo sun buga littattafai, ya kamata a basu goyon bayan da ya dace don su sami tsayawa da kafafunsu.

 

Gwamnatin Bauchi ta Kaddamar da Jami’an Sintiri 2100 Don Inganta Tsaron Dazuka da Yankunan Karkara

 

A cewar Marafa, “Mawallafa Littattafai na fuskantar kalubale a sakamakon yadda al’adar karatu tayi rauni a tsakanin jama’a, a sakamakon koma wa karatu a kan wayoyi da yanar gizo, baya ga tsadar da kayan buga Littattafan suka yi”.

 

Adan haka ya ce akwai buƙatar gwamnati ta dauki matakan da suka dace don inganta rayuwar mutane ta hanyar basu ilmi da goyon baya don a gudu tare a tsira tare.

 

Kungiyar Muryar Matan Arewa ta Sha Alwashin Wayar da Kan Al’umma Akan Illolin Shaye-shaye

 

Shima mawallafin, Malam Jibrin Mohammed Dan azumi, ya ce ya rubuta Littattafan ne bayan yin dogon nazari tare da hujjoji, harma ya bada tabbacin cewa za su amfanar da mutane musamman dalibai wajen samun ilimin da ya dace domin ciyar da al’umma gaba.

 

Sabbin Littattafan da aka kaddamar sun hadar da Gudunmawar Siyasar Musulunci wajen inganta tsaro da Zaman lafiya a Najeriya, Shawarwari akan cutar amai da gudawa a mahangar addini da zamani da kuma COVID-19 a matsayin darussa ga rayuwar musulmi, inda ake siyar da kowanne akan Naira dubu daya, a yayin da Mutane da dama suka siya don karantawa ko raba wa Makarantu.

 

NOA ta Fara Gangamin Wayar da Kan Matasan Jihar Bauchi Domin Inganta Tsaro

The post Tsohon Grand Khadi na Bauchi ya Buƙaci Gwamnati ta Bawa Mawallafa Littattafai Goyon Baya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow