Tinubu Bashi da Wani Tarihin Aikata Laifi a Amurka ko Najeriya – Omokri

Daga Bashir Gasau.   Sabon Jakadan da aka nada, Reno Omokri, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI), ta fitar da bayanan aikata laifuka kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana ikirarin a matsayin na ƙarya.   Omokri ya sanar da hakan ta cikin wani […] The post Tinubu Bashi da Wani Tarihin Aikata Laifi a Amurka ko Najeriya – Omokri appeared first on GTR .

Tinubu Bashi da Wani Tarihin Aikata Laifi a Amurka ko Najeriya – Omokri












Daga Bashir Gasau.

 

Sabon Jakadan da aka nada, Reno Omokri, ya yi watsi da rahotannin da ke cewa Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI), ta fitar da bayanan aikata laifuka kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana ikirarin a matsayin na ƙarya.

 

Omokri ya sanar da hakan ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce kasancewar bayanan mutum a kundin FBI ba lallai ba ne ya nuna cewa mutumin ya aikata laifi.

 

Kwamishinan Matasa na Jihar Borno ya yi Barazanar Guntule Yatsan Duk Wanda Yaƙi Zaɓar APC

 

Ya ƙara da cewa wasiƙar da Ofishin Jakadancin Amurka ya aika a shekarar 2003, sakamakon tambayar da tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Tafa Balogun, ya yi, ta tabbatar da cewa babu wani tarihin laifi da ya shafi Tinubu.

 

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa FBI ta miƙa wasu bayanai da suka shafi Tinubu ga Alƙali Howell Beryl na Kotun Gundumar Amurka a ranar 28 ga Agusta 2026, amma a ɓoye domin alƙalin ya duba su ba tare da fitar da su ga jama’a ba.

 

Kada ku Zaɓi APC a 2027 – Huɗubar Tsohon Minista ga ’Yan Najeriya

The post Tinubu Bashi da Wani Tarihin Aikata Laifi a Amurka ko Najeriya – Omokri appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow