SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu

Rubutun Dakta Nura Garba.   Shirin Inganta Ƙwarewa domin Bunƙasa Rayuwa da Samar da Ci-gaba wato Skills Improvement to Boost Livelihood and Nurture Growth (SIBLING), da ake gudanarwa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya zama wani abin koyi wajen amfani da haɗin guiwar jami’o’i da ɓangarori masu zaman kansu wajen magance matsalolin rashin aikin yi, […] The post SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu appeared first on GTR .

SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu


















Rubutun Dakta Nura Garba.

 

Shirin Inganta Ƙwarewa domin Bunƙasa Rayuwa da Samar da Ci-gaba wato Skills Improvement to Boost Livelihood and Nurture Growth (SIBLING), da ake gudanarwa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya zama wani abin koyi wajen amfani da haɗin guiwar jami’o’i da ɓangarori masu zaman kansu wajen magance matsalolin rashin aikin yi, ƙarancin abinci da gibin da ke tsakanin ilimin aji da kuma aiwatarwa a aikace.

 

Shirin, wanda Ƙungiyar Mata Manoma ta Najeriya (WOFAN) ke jagoranta tare da haɗin guiwar jami’ar Bayero ta hannun Cibiyar Nazarin Noma a Yankunan Tsandauri wato Centre for Dryland Agriculture (CDA), da kuma Tsangayar Aikin Gona, yana mayar da hankali wajen bawa ɗalibai ilimin aikin gona a aikace, maimakon koyarwa a aji kawai.

 

Haka kuma shirin yana koya wa ɗalibai dabarun noman zamani, gudanar da kasuwancin aikin gona, ƙara darajar amfanin gona da kuma harkokin kasuwanci, domin su sami damar dogaro da kansu bayan kammala karatu.

 

Wannan tsari yana taimaka wa ɗalibai su fahimci cewa aikin gona ba kawai aikin amfani da Fartanya da Garma ba ne, illa sana’a ce ta zamani wadda za ta iya samar da riba, aiyukan yi da kuma ci-gaban tattalin arziki.

 

Sarkin Rano ya Ɗaga Darajar Wasu Dagatai Biyu Zuwa Hakimai

 

SIBLING ya wuce iyakokin Jami’ar Bayero, domin yana bayar da hanyar magance matsalar rashin aikin yi ga masu digiri, ƙarancin amfanin gona, aiyukan faɗaɗa ilimin noma da kuma rashin samun damar ɗalibai na fuskantar harkokin kasuwanci kai tsaye.

 

SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu

 

A cewar Dakta Salamatu Garba, “Jami’o’i ya kamata su zama cibiyoyin kirkire-kirkire, samar da kasuwanci, maimakon cibiyoyin da ke ba da takardun shaidar kammala karatu kawai”.

 

Ɗaya daga cikin manyan nasarorin shirin shi ne haɗin guiwar da ke tsakanin WOFAN da BUK, inda WOFAN ke samar da kayan aikin gona, Injina, ababen more rayuwa da tallafin fasaha, yayin da jami’ar ke samar da filaye, ƙwarewar fasaha da goyon bayan hukumomi.

 

Haɗin guiwar ta kuma ƙunshi bincike, ilimi ga gwamnati da bangarori masu zaman kansu, tare da samar da yanayin da ɗalibai za su iya koyon yadda ake ƙirƙirar aiyukan yi maimakon dogaro da neman aiki kawai.

 

Makura ga Aiyukan Alheri: Juyin Juya Halin Tausayi, Haɗin Guiwa Don Wadata Kowa na Dakta Salamatu Garba – Lamarah Garba

 

Irin wannan gogewa tana ƙara wa ɗalibai ƙwarin guiwa, tana inganta damar samun aikin yi, tare da sanyawa su fahimci aikin gona a matsayin kasuwanci mai riba.

 

SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu

 

Gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun nuna sha’awarsu ga shirin, musamman a lokacin ziyarar da Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, da Ministar Kasa a Ma’aikatar Ilimi, Farfesa Suwaiba Said Ahmad, suka kai Jami’ar saboda irin muhimmancin da Gwamnatin Tarayya ke ba shi.

 

Haka kuma, Ƙungiyar Ɗaliban Jami’ar Bayero ta yaba da shirin, tana mai nuna cewa ilimin aikace-aikace yana da matuƙar muhimmanci wajen shirya ɗalibai domin fuskantar ƙalubalen tattalin arzikin da za a iya fuskanta a gaba

 

Nasarar SIBLING ta nuna cewa jami’o’in Najeriya ya kamata su ƙara neman haɗin guiwa da ƙungiyoyin masu zaman kansu, hukumomin raya ƙasa da kamfanonin aikin gona domin cike gibin da ke tsakanin ilimi da kuma aiwatarwa a aikace.

 

WOFAN ta yi Bikin Yaye Dalibai Tare da Karrama Masu Hazaka, Inda ta Nemi Ƙara Ƙarfafa Haɗin Guiwa Tsakanin Iyaye da Makaranta

 

Ya kamata jami’o’in tarayya, jihohi da masu zaman kansu da ke koyar da aikin gona, kimiyyar muhalli da sauran fannoni masu alaƙa su nazarci shirin SIBLING tare da daidaita shi da yanayin yankunansu.

 

Irin wannan haɗin guiwa na iya sauya gonakin jami’o’i zuwa cibiyoyin bincike, samar da amfanin gona na kasuwanci, kirkire-kirkire da koyar da harkokin kasuwanci.

 

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), ma’aikatun da abin ya shafa da majalisun gudanarwar jami’o’i ya kamata su samar da manufofin da za su ƙarfafa irin waɗannan haɗin guiwar tsakanin jami’o’i da masana’antu.

 

Yayin da Najeriya ke fama da ƙarancin abinci da rashin aikin yi tsakanin matasa, ya zama wajibi Majalisar Ƙasa ta gaggauta dubawa tare da amincewa da kudirin ƙarfafa aiyukan faɗaɗa ilimin noma (Agricultural Extension Bill), domin ingantaccen tsarin faɗaɗa ilimin noma zai taimaka wajen haɗa jami’o’i, cibiyoyin bincike, ƙwararrun masu faɗaɗa ilimin noma, manoma da masu zaman kansu, domin sabbin fasahohi su isa ga manoma.

 

Ministan Ilimi ya Yabawa Shirin WOFAN–CDA SIBLING, ta Hanyar Jinjinawa Ƙoƙarin Inganta Ƙwarewar Ɗaliban Aikin Gona da Horo na Aikace-aikace

 

Marubucin ya yi yabo na musamman ga Shugabar Ƙungiyar Mata Manoma ta Najeriya (WOFAN), Dakta Salamatu Garba (Ambasadar Zaman Lafiya), saboda hangen nesanta da jajircewarta wajen amfani da aikin gona wajen ƙarfafa mata, matasa da al’ummomin da ke cikin yanayi na rauni.

 

Bugu da kari Shirin SIBLING ya sake tabbatar da cewa saka jari ga mutane na iya haifar da babban sauyi, domin yana taimaka wa ɗalibai samun ƙwarewar aiki, dabarun kasuwanci da ilimin gudanar da harkokin kasuwanci.

 

A ƙarshe ya ce shirin SIBLING ba shirin aikin gona ba ne kawai, illa abin koyi ne wajen gyaran ilimi, ƙarfafa tattalin arziki da samar da ci-gaba mai ɗorewa, inda ya kamata Najeriya ta yaɗa irin wannan tsari zuwa sauran manyan cibiyoyin ilimi domin ƙarfafa matasa, ƙara samar da abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

 

Sharhi: Jami’in Sashen Sadarwa na Cibiyar Nazarin Noma a Yankunan Tsandauri na Jami’ar Bayero ta Kano, Dakta Nura Garba.

 

Gwamnan Bauchi ya Buƙaci Rundunar Sojin Najeriya ta Kafa Sabuwar Bataliya a Yankin Alkaleri

The post SIBLING: Abin Koyi ga Kasa Wajen Farfaɗo da Ilimin Aikin Gona ta Hanyar Haɗin Guiwar Gwamnati da Bangarori Masu Zaman Kansu appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow