Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, ya Taya Gwamnan Kano da Musulmin Duniya Murnar Bikin Maulidi

Daga Bashir Gasau.   Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice dake Kano, Auwal Lawal Muhammad (Dan Malikin Garo), ya taya gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da al’ummar jihar dama Musulmin duniya murnar bikin Maulidin, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.   Dan Malikin Garo, ya yaba wa gwamnan a bisa kokarinsa na hada kan al’ummar […] The post Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, ya Taya Gwamnan Kano da Musulmin Duniya Murnar Bikin Maulidi appeared first on GTR .

Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, ya Taya Gwamnan Kano da Musulmin Duniya Murnar Bikin Maulidi












Daga Bashir Gasau.

 

Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice dake Kano, Auwal Lawal Muhammad (Dan Malikin Garo), ya taya gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da al’ummar jihar dama Musulmin duniya murnar bikin Maulidin, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

 

Dan Malikin Garo, ya yaba wa gwamnan a bisa kokarinsa na hada kan al’ummar jihar musamman abinda ya shafi addini, domin magance rarrabuwar kawuna da fahimtar juna domin kawo zaman lafiya.

 

WOFAN ta Ziyarci Birnin Kigali na Ƙasar Rwanda Domin Ƙaruwa da Hanyoyinta na Ilmantarwa, Hanyoyin Zurfafa Sulhu ta Dabarun Shugabanci

 

A cewarsa, “Wannan Lokaci ya kasance wanda al’umma za suyi amfani da shi wajen kara neman kusanci da Allah, tare da addu’oin neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan jiha da ƙasa baki daya”.

 

A ƙarshe ya ce Gwamna Yusuf ya cancanci yabo a bisa sadaukarwa da tsantsar tausayin da yake nunawa al’umma musamman a fannin lafiya, la’akari da yadda yake gyarawa da inganta Asibitoci, samar da kayan aikin likitanci na zamani harma da horas da ma’aikatan lafiya.

 

Gwamnan Kano Bai da Mashawarta na Gari, Injiniya Sagir Koki Kuma Bai San Masoyansa na Gaske ba – Ambasada Sunusi Balarabe

The post Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice, ya Taya Gwamnan Kano da Musulmin Duniya Murnar Bikin Maulidi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow