RUSHEWAR GINI A UNGUWAR GAIDA: Lauyoyi Sun Bukaci ’Yan Sanda Su binciki Lamarin

Daga Bashir Gasau.   Ofishin Lauyoyi na Bashir Yusuf Tudunwazirchi & Associates, ya shigar da koke ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, yana neman a gudanar da cikakken bincike kan rushewar wani gini mai hawa uku da ba a kammala ba a unguwar Gaida, da ke karamar hukumar Kumbotso.   Lauyoyin sun shigar da koken […] The post RUSHEWAR GINI A UNGUWAR GAIDA: Lauyoyi Sun Bukaci ’Yan Sanda Su binciki Lamarin appeared first on GTR .

RUSHEWAR GINI A UNGUWAR GAIDA: Lauyoyi Sun Bukaci ’Yan Sanda Su binciki Lamarin












Daga Bashir Gasau.

 

Ofishin Lauyoyi na Bashir Yusuf Tudunwazirchi & Associates, ya shigar da koke ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, yana neman a gudanar da cikakken bincike kan rushewar wani gini mai hawa uku da ba a kammala ba a unguwar Gaida, da ke karamar hukumar Kumbotso.

 

Lauyoyin sun shigar da koken ne a madadin wani, Alhaji Surajo Yusuf, wanda ya ce ya rasa dansa sakamakon rushewar ginin.

 

Gidauniyar Dangote ta Karɓi Ragamar Cibiyar Koyon Sana’o’i ta Dangote Daga Gwamnatin Kano na Tsawon Shekaru 20

 

A cewar takardar koken, Iftila’i ya faru ne a ranar 15 ga Agusta, 2026, lokacin da ginin ya rushe ba zato, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane tare da jikkata wasu.

 

Lauyoyin sun ce kafin faruwar lamarin, mazauna yankin da makwabta sun sha jan hankalin mamallakin ginin kan wasu matsaloli da ake zargin an lura da su, ciki har da yadda aka tsara ginin da kuma yadda ake gudanar da aikin.

 

Sun kuma yi zargin cewa an gargadi mamallakin ginin kan yiwuwar rushewar ginin idan ba a dauki matakin gaggawa wajen magance matsalolin da aka gano ba.

 

Wani Matashi ya Mayar da Naira Dubu 300n da ya Tsinta a Kano

 

Saboda haka, lauyoyin sun bukaci ’yan sanda su gudanar da bincike kan Alhaji Ali Nagarta, musamman kan yadda aka gudanar da aikin ginin, da yadda aka kula da shi, da kuma matakan sa ido da aka dauka yayin aikin.

 

Daga cikin abubuwan da lauyoyin suka bukaci a gudanar da bincike a kansu akwai musabbabin rushewar ginin, rawar da mutanen da ke da hannu wajen ginin suka taka, da kuma alhakin da ya rataya a kansu wajen gine-gine, kulawa da kuma sa ido.

 

Adan haka suka bukaci a gayyaci tare da yi wa duk mutanen da ke da muhimman bayanai game da ginin da gargadin da ake zargin an yi wa mamallakin ginin.

 

Gaskiyar Lamari Kan Yadda Ƙasashen Duniya Suka Sanyawa Arzikin Najeriya Ƙahon Zuƙa – Abdulkarim Daiyabu

 

An dai aike da Kwafin takardar koken ga ofishin gwamnan Kano da hukumar kare hakkin Dan’adam ta ƙasa da kuma ofishin kwamishinan shari’a na Kano.

 

Lauyoyin sun ce idan binciken ya tabbatar da cewa akwai mutanen da suka aikata laifin da ya dace da hukunci, ya kamata a dauki matakin shari’a a kansu bisa tanadin doka.

 

A ƙarshe sun ce daukar matakin gaggawa na da muhimmanci, musamman ganin asarar rayukan da lamarin ya haddasa da kuma bukatar daukar matakan da za su hana sake faruwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.

 

Tinubu ne Dan Takara ta a Zaɓen 2027 – Gwamnan Osun na Jam’iyyar Accord

The post RUSHEWAR GINI A UNGUWAR GAIDA: Lauyoyi Sun Bukaci ’Yan Sanda Su binciki Lamarin appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow