Ranar Yawan Al’umma ta Duniya: Yawan Mutanen Duniya ya kai Bilyan 8.2 – Madawakin Muri

Daga Kallamu Galadima Dambo.   A ranar 11 ga watan Yulin kowacce shekara, Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Yawan Al’umma ta Duniya.   Manufar ware ranar shine domin tunatar da mutane game da yawa da rabe-raben shekaru da kuma buƙatun yawan al’ummar duniya baki daya, a samakon mahimmancinsu ga mafi yawancin harkokin […] The post Ranar Yawan Al’umma ta Duniya: Yawan Mutanen Duniya ya kai Bilyan 8.2 – Madawakin Muri appeared first on GTR .

Ranar Yawan Al’umma ta Duniya: Yawan Mutanen Duniya ya kai Bilyan 8.2 – Madawakin Muri












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

A ranar 11 ga watan Yulin kowacce shekara, Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Yawan Al’umma ta Duniya.

 

Manufar ware ranar shine domin tunatar da mutane game da yawa da rabe-raben shekaru da kuma buƙatun yawan al’ummar duniya baki daya, a samakon mahimmancinsu ga mafi yawancin harkokin yau da kullum.

 

Akwai Damuwa Kan Tsarin Tarbiyya da Zamantakewar Dalibai A Makarantun Jihar Bauchi – Kwamishinan Ilimi

 

Da yake zantawa da GTR Hausa, tsohon Darakta a hukumar Kidaya ta Najeriya, Dakta Inuwa Bakari Jalingo (Madawakin Muri), ya ce a halin yanzu ƙididdiga ta nuna cewa yawan al’ummar Duniya ya kai Mutum Bilyan 8.2.

 

Ranar Yawan Al'umma ta Duniya: Yawan Mutanen Duniya ya kai Bilyan 8.2 - Madawakin Muri

 

Dadin dadawa ya ce a halin yanzu Najeriya na da mutum sama da Milyan 230, a sakamakon yadda aka shafe shekaru masu yawa ba a yi kidaya a ƙasar ba.

 

APC ta Tabbatar da Kashim Shettima a Matsayin Abokin Takarar Tinubu a Zaben 2027

 

Ya kara da cewa manufar kirkirar wannan rana shine tunatar da al’umma amfanin yawan al’umma a kasa da kuma illar rashin kula dasu.

 

Taken ranar na bana shine “Lura da rayuwar matasa ta hanyar basu ingantacciyar kulawa domin samun goben kasa me kyau.

 

Muhammad ya Sake Zama Sunan da Aka fi Sanya wa Jarirai a Ingila da Wales

 

Adan haka ya ce bawa Matasan kasar nan kulawa ta musamman a sha’anin Ilimi, Lafiya, da samar musu da kayan more rayuwa na a Matsayin abinda zai inganta kasar a kowanne mataki.

 

A karshe ya yi fatan gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki za su bawa harkokin Matasa fifiko, ta yadda zai zaman Najeriya ta dada bunkasa a kowanne bangare.

 

Karin Hasken Lauyan Jam’iyyar ADC na Kasa Kan Gargaɗi ga Rassansu na Jihohi Dangane da Shari’un da Suka Shafi Jam’iyyar

The post Ranar Yawan Al’umma ta Duniya: Yawan Mutanen Duniya ya kai Bilyan 8.2 – Madawakin Muri appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow