NEMA da SEMA Sun Shirya Taron Wayar da Kan Jama’a Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa a Kano

Daga Bashir Gasau.   Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), da hadin guiwar takwararta ta jihar Kano (SEMA), sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki don wayar da kan al’ummomin yankunan da ke cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa.   Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA), Jamil Sagir Danbala, ne ya […] The post NEMA da SEMA Sun Shirya Taron Wayar da Kan Jama’a Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa a Kano appeared first on GTR .

NEMA da SEMA Sun Shirya Taron Wayar da Kan Jama’a Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa a Kano

Daga Bashir Gasau.

 

Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), da hadin guiwar takwararta ta jihar Kano (SEMA), sun gudanar da taron masu ruwa da tsaki don wayar da kan al’ummomin yankunan da ke cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa.

 

Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA), Jamil Sagir Danbala, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce taron na a matsayin wani ɓangare na Gangamin Ƙasa, kan Shirin tunkarar ambaliya da isar da saƙon gargaɗi ga al’umma.

 

Rahoto: Kotu ta Umarci a Kamo Aliyu Haidar Kan Zargin Siyar da Kadarorin Bogi na Milyan 134 a Kano

 

A yayin taron, mahalartan sun jaddada muhimmancin haɗin kan gwamnati da al’umma, wajen rage illolin ambaliyar ruwa da ke haddasa asarar rayuka, dukiyoyi da lalata ababen more rayuwa.

 

NEMA da SEMA Kano sun kuma yi kira ga daukacin al’umma, shugabannin gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, dasu mara wa gwamnati baya wajen aiwatar da matakan kariya da kuma bin shawarwarin da hukumomi ke bayarwa.

 

Gwamnan Yobe ta Zaftare wa Manoma Kashi 50 na Kudin Hayar Taraktocin Noma

 

Ga jerin shawarwarin da hukumomin suka bawa mahalarta taron da sauran al’ummar jihar Kano:

 

1. A rika sharewa da kwashe dagwalon shara daga magudanan ruwa kafin da kuma lokacin damina

 

2. A guji yin gine-gine a hanyoyin ruwa da wuraren da ke fuskantar haɗarin ambaliya

 

3. Gina ingantattun magudanan ruwa a gaban gidaje da wuraren kasuwanci

 

4. A guji amfani da kayan gini marasa inganci

 

5. Rufe magudanan ruwa yadda ya kamata tare da kula da su akai-akai

 

Babu Dalilin Barin Shugabannin da Muka San Gafiya ta Fisu Hankali – Abdulkarimu Daiyabu

 

6. Hana yara yin wanka a kududdufai, rafuka da wuraren da ruwa ya mamaye

 

7. Sare rassan bishiyoyi da ka iya taɓa layukan wutar lantarki

 

8. Kada a tare hanyoyin shiga da fita da jami’an ceto ka iya amfani da su yayin ayyukan gaggawa

 

9. Kai rahoton duk wani lamarin gaggawa ta waɗannan lambobin: Red Cross: 112 ko na Hukumar Kashe Gobara ta Kano 07026026400 da kuma 08107888878.

 

A ƙarshe an bayyana cewa ƙananan hukumomi 28 na Jihar Kano, na cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa matuƙar ba a ɗauki matakan kariyar da suka dace ba.

 

Taron ya sami halartar masu ruwa da tsaki, kamar wakilan Red Cross, NiMet, Ma’aikatar Muhalli, jami’an tsaro, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Kano, wakilan ƙungiyoyi, da sauran shugabannin al’umma.

 

Kungiyar CAN ta Bukaci Gwamnatin Najeriya ta Sanya Dokar ta Baci a Sha’anin Tsaron Kasar

The post NEMA da SEMA Sun Shirya Taron Wayar da Kan Jama’a Kan Matsalar Ambaliyar Ruwa a Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow