NBA (Ungogo Branch) Kano ta Bukaci Shugaba Tinubu ya Magance Matsalar Tsaron Najeriya

Daga Bashir Gasau.   Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Ungogo da ke jihar kano, ta buƙaci fadar shugaban kasa ta magance matsalar rashin tsaro a kasar.   Shugaban Kungiyar, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe, ne ya baiyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya […] The post NBA (Ungogo Branch) Kano ta Bukaci Shugaba Tinubu ya Magance Matsalar Tsaron Najeriya appeared first on GTR .

NBA (Ungogo Branch) Kano ta Bukaci Shugaba Tinubu ya Magance Matsalar Tsaron Najeriya

Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Ungogo da ke jihar kano, ta buƙaci fadar shugaban kasa ta magance matsalar rashin tsaro a kasar.

 

Shugaban Kungiyar, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe, ne ya baiyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada-kai wajen yaki da rashin tsaro tare da mutunta doka, da bin hanyoyin da suka dace domin gina kasa mai cike da zaman lafiya, adalci da ci-gaba.

 

Gwamnan Kano ya Dakatar da Shugabar Hukumar Tsara Birane (KNUPDA)

 

A cewar Gwadabe, “Rashin tsaro na ci-gaba da kasancewa daya daga cikin manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta ta fuskar ta’addanci, satar mutane, da sauran laifukan da suka shafi al’umma da tattalin arzikin kasa”.

 

A wannan yanayi akwai bukatar shugabanni da kwararru daga fannoni daban-daban su taka muhimmiyar rawa wajen bayar da gudunmawa ga zaman lafiya da tabbatar da adalci.

 

Jam’iyyar Action Alliance ce Jirgin Fiton Talakawan Najeriya – Ma’ajin Jam’iyyar na Kasa

 

Ya kara da cewa yaki da rashin tsaro ba aikin jami’an tsaro kadai ba ne, saboda haka ya zama wajibi a sami hadin guiwa tsakanin gwamnati, bangaren shari’a, kungiyoyin farar hula da kuma al’umma domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

 

A karshe ya jaddada cewa mutunta doka, kare hakkin dan Adam, samar da adalci cikin gaggawa suna daga cikin ginshikan da za su taimaka wajen dawo da amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati da na tsaro.

 

Shelkwatar Tsaron Najeriya ta Magantu Kan Rasuwar Janar Rabe a Hannun ‘Yan Bindiga

The post NBA (Ungogo Branch) Kano ta Bukaci Shugaba Tinubu ya Magance Matsalar Tsaron Najeriya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow