Miyetti Allah Kautal Hore ta Gargaɗi Fulani Kan Ɗaukar Makamai a Lokacin Shagulgulan Sallah

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya (Miyetti Allah Kautal Hore), ta gargaɗi Fulanin kasar da su guji ɗaukar Makamai a lokacin shagulgulan bikin babbar Sallah.   Shugaban kungiyar na shiyyar Arewa ta tsakiya, Alhaji Gidado Idris Bebeji, ne ya baiyana hakan a yayin taron da ƙungiyar ta shirya kan tsare-tsaren bikin […] The post Miyetti Allah Kautal Hore ta Gargaɗi Fulani Kan Ɗaukar Makamai a Lokacin Shagulgulan Sallah appeared first on GTR .

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Najeriya (Miyetti Allah Kautal Hore), ta gargaɗi Fulanin kasar da su guji ɗaukar Makamai a lokacin shagulgulan bikin babbar Sallah.

 

Shugaban kungiyar na shiyyar Arewa ta tsakiya, Alhaji Gidado Idris Bebeji, ne ya baiyana hakan a yayin taron da ƙungiyar ta shirya kan tsare-tsaren bikin sallar a tsakanin ‘ya’yansu.

 

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta Cika Shekaru 63 da Kafuwa

 

A cewarsa, “Makasudin taron shi ne kira ga iyayen Makiyaya dama hukumomin Najeriya domin tabbatar da babu wani Bafulatani da ya ɗauki Adda, Sanda ko kuma dukkan wani nau’in makami a yayin bikin Sallah”.

 

Ya kuma baiyana buƙatar da ke akwai wajen ganin an bar ‘ya’yan Fulani Makiyaya sun gudanar da bikin Sallah ba tare da tsangwama ba, kamar yadda sauran Ƙabilu ke nasu ruguntsumin a lokutan bikin Sallah dama sauran bukukuwan da ake gudanarwa lokaci bayan lokaci.

 

Hotuna: Yadda Mahajjata ke Tafiya Filin Mina Domin Gudanar da Aikin Hajjin Bana

 

Daga bisani Gidado Bebeji ya bayyana haɗin-kai a tsakanin jagororin makiyaya a matsayin mafita ga rikice-rikicen da ke yawaita faruwa, musamman a tsakanin Manoma da Makiyaya a Najeriya.

 

Dakta Musa Adamu Labaran na Jami’ar Bayero ta Kano ya Rasu

 

Alhaji Hassan Amfana dake a matsayin tsohon jami’in dan sanda kana daya daga cikin dattawan Makiyayan da suka halarci taron daga jihar Plateau, ya roki mahukuntan jiharsa dama na gwamnatin tarayya da su ɗauki matakan tabbatar da zaman lafiya a tsakanin makiyayan jihar da na Najeriya baki ɗaya.

 

Taron ya gudana ne a garin Maraba na ƙaramar hukumar Karu da ke jihar Nasarawa, inda ya sami halartar Makiyaya daga sassar jihar dama wasu jihohin Najeriya.

 

Bidiyo: Rahoton Ziyarar GMBNI a Tsangayar Malam Umar Bagobiri Dake Jihar Nasarawa

The post Miyetti Allah Kautal Hore ta Gargaɗi Fulani Kan Ɗaukar Makamai a Lokacin Shagulgulan Sallah appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow