Matsalar Shaye-shaye na Bukatar Ayi Mata Taron Dangi Wajen Murƙusheta – NOA Kano

Daga Usman Hamza Kano.   Hukumar wayar da kan Al’umma ta Najeriya (NOA) reshen jihar Kano, ta ce dole sai anyi wa matsalar sheye-shaye taron dangi matuƙar ana son murƙusheta.   Shugabar Sashen hulɗa da ‘Yan Jaridu da wayar da kan jama’a ta hukumar a jihar, Hajiya Hauwa Adamu Garba, ce baiyana hakan a yayin […] The post Matsalar Shaye-shaye na Bukatar Ayi Mata Taron Dangi Wajen Murƙusheta – NOA Kano appeared first on GTR .

Matsalar Shaye-shaye na Bukatar Ayi Mata Taron Dangi Wajen Murƙusheta – NOA Kano

Daga Usman Hamza Kano.

 

Hukumar wayar da kan Al’umma ta Najeriya (NOA) reshen jihar Kano, ta ce dole sai anyi wa matsalar sheye-shaye taron dangi matuƙar ana son murƙusheta.

 

Shugabar Sashen hulɗa da ‘Yan Jaridu da wayar da kan jama’a ta hukumar a jihar, Hajiya Hauwa Adamu Garba, ce baiyana hakan a yayin zantawarta da Guarantee Radio Kano, inda ta ce akwai matuƙar bukatar hadin guiwa a tsakanin Iyaye, Shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki don tunkarar matsalar wadda ta addabi Mata da Matasa.

 

Dole Tinubu ya Bayyana Mana Dalilin Korar Ministocinsa Guda Biyu – Dino Melaye

 

Adan haka ta ce Hukumar a Kano ta yi wani yunƙuri na shirya gangamin wayar da kan Al’umma akan Illolin Shaye-shaye, ta hanyar hadin guiwa da hukumar hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA).

 

A nata bangaran daya daga cikin manyan Jami’an NDLEA a Kano, ASC Maimuna Garba Muhammad, ta buƙaci masu ruwa da tsakin jihar da su kafa kwamiti Mai ƙarfi don yakar Ɗabi’ar, la’akari da yadda hukumarsu ke aiki tukuru wajen ganin an daƙile matsalar duk da cikas din da wasu Bata-garin cikin al’umma ke kawo musu.

 

A ƙarshe hukumomin biyu sun ce yanzu haka suna ci-gaba da yin gangamin yaki da shan miyagun ƙwayoyi a kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano.

 

Gwamna Yusif ya Aikawa Majalisar Dokokin Kano Sunan Murtala Sule Garo, Domin ta Tantance Shi a Matsayin Mataimakinsa

The post Matsalar Shaye-shaye na Bukatar Ayi Mata Taron Dangi Wajen Murƙusheta – NOA Kano appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow