Ma’aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Sun Gudanar da Zanga-zanga Bisa Kin Kara Musu Albashi

Daga Abdurrashid B. Imam.   A safiyar yau Alhamis, 25 ga watan Yunin shekarar 2026, ne Ma’aikatan Kamfanin yin Buhu na (BAGCO), da ke rukunin Kamfanonin Sharaɗa ta jihar Kano, suka gudanar da Zanga-zanga tare da hana dukkan shugabannin da ma’aikata shiga Kamfanin.   Ma’aikatan sun ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon yadda mahukuntan […] The post Ma’aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Sun Gudanar da Zanga-zanga Bisa Kin Kara Musu Albashi appeared first on GTR .

Ma’aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Sun Gudanar da Zanga-zanga Bisa Kin Kara Musu Albashi












Daga Abdurrashid B. Imam.

 

A safiyar yau Alhamis, 25 ga watan Yunin shekarar 2026, ne Ma’aikatan Kamfanin yin Buhu na (BAGCO), da ke rukunin Kamfanonin Sharaɗa ta jihar Kano, suka gudanar da Zanga-zanga tare da hana dukkan shugabannin da ma’aikata shiga Kamfanin.

 

Ma’aikatan sun ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon yadda mahukuntan Kamfanin suka gaza cika musu alkawarin da suka yi musu a watan Mayu na kara musu albashi a wannan wata na Yuni.

 

Jami’an Tsaron Jamhuriyar Nijar Sun Kama Dan Najeriya Dake Hada-hadar Kudaden Jabu

 

A cewarsu, “A karshen watan da ya wuce mun gudanar da Zanga-zanga kan kara mana albashi, amma suka kira jagororin Kamfanin daga jihar Legas, kuma suka ce mana mu yi hakuri za su kara mana a karshen watan nan na Yuni”.

 

Ma'aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Suka Gudanar da Zanga-zanga Bisa Kin Kara Musu Albashi

 

“Toh sai dai kuma a jiya Laraba ne suka tara mu suka shaida mana cewa babu maganar kara mana albashin a wannan wata, sai dai mu jira zuwa wani lokaci da basu sanar mana ba”.

 

Hotuna: Yadda Ma’aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Suka Gudanar da Zanga-zanga

 

Sun kara da cewa tun watanni 15 da suka wuce suka yi musu alkawarin karin albashi, amma sun gaza cika alkawarin, illa karin da suka yi wa Injiniyoyin kaɗai.

 

Ma'aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Suka Gudanar da Zanga-zanga Bisa Kin Kara Musu Albashi

 

Akan wannan Zanga-zanga, GTR Hausa ta tuntubi Manajan Kamfanin BAGCO na jihar Kano, Alhaji Tijjani Isyaku, amma ya ce ba zai ce komai ba, inda ta tura wakilinmu, Abdurrashid B. Imam, wajen jami’in da ke kula da ma’aikata amma shima ya ƙi cewa uffan.

 

AIG Zone One da Dala Inland Dry Port za su yi Haɗin Guiwa Don Inganta Tsaro da Tattalin Arziƙin Kano

 

A karshe Ma’aikatan Kamfanin sun roki Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, da dukkan masu ruwa da tsaki akan su kawo musu dauki akan wannan turka-turka da ke tsakaninsu da Kamfanin nasu.

 

Majalisar Dattawan Najeriya ta Amince da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi

The post Ma’aikatan Kamfanin BAGCO na Kano Sun Gudanar da Zanga-zanga Bisa Kin Kara Musu Albashi appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow