Kungiyar MACBAN ta Bukaci a Gudanar da Cikakken Bincike Kan Harin da Bata-gari Suka Kai Kauyen Otukpo-Nobi na jihar Benue

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi Allah-Wadai da Harin da wasu bata gari suka kai a yankin Otukpo-Nobi, dake jihar Benue a Arewa ta tsakiyar Najeriya.   Sakataren kungiyar na jihar Benue, Alhaji Ibrahim Galma, ne ya sanar da hakan ta cikin wata […] The post Kungiyar MACBAN ta Bukaci a Gudanar da Cikakken Bincike Kan Harin da Bata-gari Suka Kai Kauyen Otukpo-Nobi na jihar Benue appeared first on GTR .

Kungiyar MACBAN ta Bukaci a Gudanar da Cikakken Bincike Kan Harin da Bata-gari Suka Kai Kauyen Otukpo-Nobi na jihar Benue












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi Allah-Wadai da Harin da wasu bata gari suka kai a yankin Otukpo-Nobi, dake jihar Benue a Arewa ta tsakiyar Najeriya.

 

Sakataren kungiyar na jihar Benue, Alhaji Ibrahim Galma, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwar da ya aiko wa GTR Hausa a yau Litinin, inda ya ce suna Allah-wadai da duk wani nau’in tashin hankali, tare da jaddada muhimmancin gano gaskiyar abin da ya faru, ta hanyar bincike mafi dacewa wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

 

Hukuncin Kotu Bai Shafi Ƴan Takarar da Muka Tsayar ba — ADC

 

A cewar GALMA, “Kungiyar MACBAN reshen Jihar Benuwai ta yi Allah-wadai da harin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane a yankin Otukpo-Nobi da ke Ƙaramar Hukumar Otukpo, tare da yin kira ga jama’a da su guji ɗora wa kowanne ɓangare alhakin lamarin kafin hukumomin tsaro su kammala bincikensu”.

 

Haka zalika ya ce tun a shekarar da ta gabata an kori Fulani mazauna yankin Otukpo da kewaye, ciki har da shugaban al’ummarsu, Chairman Yenusa, wanda daga bisani ya bar jihar bayan ƙoƙarin sasanta rikicin da aka yi bai yi nasara ba.

 

INEC ta Musanta Labarin Dora Bayanan ‘Yan Takarar ADC na Tsagin Nafi’u Bala a Shafinta

 

Sanarwar ta kuma ce ta sami rahotannin da ke cewa an kashe wasu mutane a ƙauyen Akpachi da ke yankin Ugboju, sai dai ta bayyana cewa har yanzu babu tabbatacciyar hujjar da ke tabbatar da yawan waɗanda suka rasa rayukansu ko cikakken yadda lamarin ya faru.

 

Ƙungiyar ta yi kira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita ko zarge-zargen da ba su da hujja, musamman waɗanda ke danganta harin da kisan marigayi Ardo Risku Mohammed, tana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga binciken da hukumomin tsaro ke gudanarwa.

 

Hotuna: Yadda Aka Shiryawa Tsohon Shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, Taron Addu’oi a Abuja

 

Bugu da kari ta buƙaci masu amfani da kafafen sada zumunta da su rinƙa tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa, tana mai gargadin cewa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba kan irin waɗannan lamurra na iya ƙara tayar da hankali tare da kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya.

 

A ƙarshe, ƙungiyar ta jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa.

 

Sarkin Musulmi ya Umarci Al’ummar Najeriya su Duba Jinjirin Watan Safar na Shekarar 1448

The post Kungiyar MACBAN ta Bukaci a Gudanar da Cikakken Bincike Kan Harin da Bata-gari Suka Kai Kauyen Otukpo-Nobi na jihar Benue appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow