Ku yi Amfani da Bikin Easter Wajen Nuna Ƙauna ga ‘Yan Najeriya – Sakon Rabaran Mbya ga Kiristoci

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Shugaban Majami’ar Ekilisiyar Yan’uwa na Najeriya (EYN), Rabaran Dakta Daniel Mbya, ya buƙaci Mabiya Addinin Kirista da su yi amfani da darussan da bikin Easter ya kunsa, wajen sabunta sadaukar da Kai tare da nuna Kauna ga ‘Yan Kasar.   Halin da Aka Wayi Gari Dashi a Safiyar Yau Litinin […] The post Ku yi Amfani da Bikin Easter Wajen Nuna Ƙauna ga ‘Yan Najeriya – Sakon Rabaran Mbya ga Kiristoci appeared first on GTR .

Ku yi Amfani da Bikin Easter Wajen Nuna Ƙauna ga ‘Yan Najeriya – Sakon Rabaran Mbya ga Kiristoci

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Shugaban Majami’ar Ekilisiyar Yan’uwa na Najeriya (EYN), Rabaran Dakta Daniel Mbya, ya buƙaci Mabiya Addinin Kirista da su yi amfani da darussan da bikin Easter ya kunsa, wajen sabunta sadaukar da Kai tare da nuna Kauna ga ‘Yan Kasar.

 

Halin da Aka Wayi Gari Dashi a Safiyar Yau Litinin a Yaƙin Iran da Kuma Amurka da Isra’ila 06=04=2026

 

Rabaran Daniel Mbya, ya baiyana hakan ne ta cikin sakon Muryar da ya aiko wa GTR Hausa, albarkacin ranar bikin Easter na Bana, inda ya shawarci al’umma da su baiwa jami’an tsaro hadin-kai domin samun cikakkiyar nasara.

 

A cewarsa, “Bisa ga koyarwar littafi mai tsarki da tarihi na Ekilisiya, kafin a Fara bikin Easter a duk shekara akan gudanar da Azumi na kwanaki Arba’in “Length”, wanda mabiyi zai kwashe tsawon wata guda yana nuna kaskantar da Kai tare da mika lamuransa kacokan ga Mahalicci”.

 

Masu Kutse Sun Damfari Mutane da Dama Bayan Sun Kwace Manhajar WhatsApp Ɗin Shugaban ADC na Kano

 

Haka zalika ya bukaci ‘Yan Najeriya da su ci-gaba da bawa Shugabani goyon Baya a kowanne mataki, musamman kokarin da mahukuntan ke yi wajen saita lamuran tsaron kasar.

 

A ƙarshe ya jaddada bukatar da ke akwai wajen ganin ‘Yan Kasar sun kasance masu taimakon juna, ba tare da la’akari da Bambancin Addini ko yare ko kuma yankin da mutum ya fito ba.

 

Atiku ya Zargi Gwamnatin Tinubu da Siye Wanda Yake Ikirarin Shine Halastaccen Shugaban Jam’iyyar ADC na Ƙasa

The post Ku yi Amfani da Bikin Easter Wajen Nuna Ƙauna ga ‘Yan Najeriya – Sakon Rabaran Mbya ga Kiristoci appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow