Ku Dauki Mataki Kafin Hakurin Musulmin Najeriya ya Kare – Sakon NSCIA ga Gwamnatin Tarayya

Daga Bashir Gasau.   Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta gargaɗi gwamnatin kasar da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa kafin hakurin Musulmi ya kare kan hare-haren nuna wariya da kuma tauye musu hakkoki da ake yi.   Wannan gargaɗi na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da […] The post Ku Dauki Mataki Kafin Hakurin Musulmin Najeriya ya Kare – Sakon NSCIA ga Gwamnatin Tarayya appeared first on GTR .

Ku Dauki Mataki Kafin Hakurin Musulmin Najeriya ya Kare – Sakon NSCIA ga Gwamnatin Tarayya












Daga Bashir Gasau.

 

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta gargaɗi gwamnatin kasar da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa kafin hakurin Musulmi ya kare kan hare-haren nuna wariya da kuma tauye musu hakkoki da ake yi.

 

Wannan gargaɗi na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na NSCIA, Abbas Jimoh, ya fitar a madadin majalisar wadda Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ke jagoranta.

 

Majalisar ta ce Musulmi na ci-gaba da nuna haƙuri duk da abin da ta bayyana a matsayin tsokanar da ake yi musu akai-akai. Haka kuma ta buƙaci a gaggauta tabbatar da adalci kan kisan da aka yi a jihohin Kaduna da Benue tare da binciken zargin rashin da’a da ake yi wa wasu jami’an ‘yan sanda.

 

Manhajar WhatsApp ya Fara Ƙaddamar da Sabon Tsarin Yin Rijista ba Tare da Lambar Waya ba

 

Sanarwar ta kuma buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa an kamo tare da hukunta waɗanda suka aikata munanan laifukan da suka faru a jihohin Kaduna da Benue tare da gurfanar da su a gaban kotu ba tare da wani jinkiri ba, domin kin yin hakan tamkar gayyata ce ga rashin doka da oda.

 

Har ila yau, majalisar ta yi kira ga gwamnati da ta dakile abin da ta bayyana a matsayin ci-gaba da cin mutuncin Musulunci da Musulmi a bainar jama’a, tana mai cewa hakan yana da muhimmanci domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

 

NSCIA ta kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan DPOn da ake zargi da miƙa malamar addinin Musulunci domin a ƙona ta, tare da binciken jami’in da ake zargi da gaiyatar Shugaban Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) kafin kashe shi, domin a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

 

Hotuna: Yadda Sarkin Hadejia ya Karbi Bakuncin Matar Shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu

 

Majalisar ta ce duk da cewa Musulmi na kallo ana nuna musu wariya tare da danganta su da zalunci, amma sun ci-gaba da kasancewa masu biyayya ga haɗin kan Najeriya.

 

Haka kuma NSCIA ta soki kalaman da ta danganta ga wani tsohon Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da yayi a wani shirin talabijin kai tsaye, tana mai cewa kalaman ba su da alhakin shugabanci kuma ya kamata hukumomin da suka dace su ɗauki mataki a kansu.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa, da ace wani shugaban Musulmi ne ya yi irin waɗannan kalamai, da tuni ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun gaiyace shi domin ya masa tambayoyi.

 

A ƙarshe, NSCIA ta yi watsi da zargin da wasu shugabannin Kirista suka yi na danganta Musulmi da Fulani da hare-haren satar mutane da suka faru a Jihar Oyo, harma ta ce sunayen mutanen da aka kama dangane da waɗannan laifuka sun nuna ba haka lamarin yake ba, sannan wanda aka kama bisa zargin satar mutane da kisan kai a ƙaramar hukumar Oriire Fasto ne ba Musulmi ba.

 

Za a Cire Sojoji Daga Tsarin Shugabancin NYSC a Najeriya

The post Ku Dauki Mataki Kafin Hakurin Musulmin Najeriya ya Kare – Sakon NSCIA ga Gwamnatin Tarayya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow