Ku Daina Yaudarar Talaka ta Hanyar Bashi Babur, Mota ko Fili – Saƙon CHRCDI ga ‘Yan Siyasar Najeriya

Daga Bashir Gasau.   Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta Najeriya (CHRCDI), ta baiyana damuwarta kan yadda ‘Yan Siyasar ƙasar ke Yaudarar Talakawa ta hanyar rabon Mashina, Motoci ko Filaye a lokacin siyasa.   Shugaban gudanarwar Kungiyar CHRCDI, Kwamared Tasi’u Idris Soja, ne ya baiyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR […] The post Ku Daina Yaudarar Talaka ta Hanyar Bashi Babur, Mota ko Fili – Saƙon CHRCDI ga ‘Yan Siyasar Najeriya appeared first on GTR .

Ku Daina Yaudarar Talaka ta Hanyar Bashi Babur, Mota ko Fili – Saƙon CHRCDI ga ‘Yan Siyasar Najeriya

Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta Najeriya (CHRCDI), ta baiyana damuwarta kan yadda ‘Yan Siyasar ƙasar ke Yaudarar Talakawa ta hanyar rabon Mashina, Motoci ko Filaye a lokacin siyasa.

 

Shugaban gudanarwar Kungiyar CHRCDI, Kwamared Tasi’u Idris Soja, ne ya baiyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce hakan bai kamata ba la’akari da yadda mafi yawancin Matasa basu da aikin yi ko sana’ar da za ta gina rayuwarsu.

 

Cigiyar Dattijo Malam Haruna Abubakar Rano, Mazaunin Unguwar Gobirawa

 

A cewar Soja, “Talaka baya buƙatar a ringa jefa masa abubuwan amfani na dan lokaci domin ɗauke masa hankali, domin abinda yafi buƙata shine gyara Kamfanoni don samar masa da aikin yi, koyar da sana’oi ga Mata da Matasa, tallafawa ƙananan ‘yan kasuwa, Inganta ilimi da lafiya da kuma gina tattalin arzikin da zai dogara da aiki ba Bara ba”.

 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta Bada Hutun Babbar Sallah

 

Adan haka ya ce idan gwamnati ta samar da aiki da sana’a, mutane za su iya siyan mashina da motoci da kansu cikin mutunci da kwanciyar hankali, wanda hakan ne zai cire talaka daga talaucin da ke sanya shi aikata abubuwa marasa kyau.

 

A ƙarshe Ƙungiyar ta ce lokaci yayi da talaka zai fara zaben shugabanni masu tsoron Allah, masu gaskiya da kishin ci-gaban al’umma, waɗanda basa amfani da talaucin jama’a wajen neman mulki, tunda sune za su samar da tsarin da zai dora matasa ga makoma mai kyau kuma ingatantacciya.

 

Miyetti Allah Kautal Hore ta Gargaɗi Fulani Kan Ɗaukar Makamai a Lokacin Shagulgulan Sallah

The post Ku Daina Yaudarar Talaka ta Hanyar Bashi Babur, Mota ko Fili – Saƙon CHRCDI ga ‘Yan Siyasar Najeriya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow