Ko Amupitan ya Sauka ko mu Ɗauki Matakin Ban Mamaki – ADC

Daga Bello Usman, Kano.   Jam’iyyar Hamayya ta ADC Najeriya ta buƙaci shugaban Hukumar zaɓen ƙasar (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da ya sauka daga muƙaminsa ko kuma su ɗauki matakin da zai girgiza kasar.   ADC dai ta sanar da hakan ne ta cikin wasu sabbin zarge-zarge kan shugaban hukumar, inda ta soki Amupitan kan […] The post Ko Amupitan ya Sauka ko mu Ɗauki Matakin Ban Mamaki – ADC appeared first on GTR .

Ko Amupitan ya Sauka ko mu Ɗauki Matakin Ban Mamaki – ADC

Daga Bello Usman, Kano.

 

Jam’iyyar Hamayya ta ADC Najeriya ta buƙaci shugaban Hukumar zaɓen ƙasar (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da ya sauka daga muƙaminsa ko kuma su ɗauki matakin da zai girgiza kasar.

 

ADC dai ta sanar da hakan ne ta cikin wasu sabbin zarge-zarge kan shugaban hukumar, inda ta soki Amupitan kan tsaffin bayanansa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, waɗanda suka riƙa nuna goyon bayansa ga jam’iyyar APC mai mulki.

 

Rahoton Yadda Tattaunawar Sulhu Tsakanin Amurka da Iran ta Kasance

 

Toh sai dai tuni INEC ta gargaɗi mutane kan amfani da intanet wajen bata suna da kuma aikata laifuka, ta hanyar yin amfani da bayanan bogi da yaɗa labaran ƙarya.

 

A ƙarshe sanarwar sakataren watsa labaran INEC, Adedayo Oketola, tace shugabancin Amupitan na fatan gudanar da zaɓe mai sahihanci da babu cutarwa a cikinsa.

 

Zantawar GTR Hausa ta Ƙarshe da Tsohon Shugaban AUFCDN, Marigayi Dakta Mohammed Tahir

The post Ko Amupitan ya Sauka ko mu Ɗauki Matakin Ban Mamaki – ADC appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow