Gwamnatin Kano za ta yi Auren Gata na Mutane Dubu Uku

Daga Amina Rabi’u Gwangwazo.   Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin, Injiniya Abba Kabir Yusuf, za ta gudanar da wani shiri na musamman na aurar da Zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wato maza 1,500 da mata 1,500.   Babban Kwamandan Hisba na Jihar Kano, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya sanar da hakan ta […] The post Gwamnatin Kano za ta yi Auren Gata na Mutane Dubu Uku appeared first on GTR .

Gwamnatin Kano za ta yi Auren Gata na Mutane Dubu Uku

Daga Amina Rabi’u Gwangwazo.

 

Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin, Injiniya Abba Kabir Yusuf, za ta gudanar da wani shiri na musamman na aurar da Zawarawa da ’yan mata dubu uku (3,000), wato maza 1,500 da mata 1,500.

 

Babban Kwamandan Hisba na Jihar Kano, Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce wannan shiri ya fi karkata ne ga marayu da kuma ’ya’yan talakawa domin tallafa musu su samu rayuwa mai inganci ta hanyar aure.

 

Kotu ta Hana INEC Amincewa da Tarukan Jam’iyyar ADC

 

Abubuwan da aka tanada ga ma’auratan sun haɗa da:

 

1. Kayan ɗaki: Gado, Sif, Madubi, Katifa, Filo da Zanin Gado.

 

2. Kayan abinci: Shinkafa, Taliya, da man girki.

 

3. Kayan sawa ga mata: Atamfa da Hijabi.

 

4. Kayan sawa ga maza: Shadda da Hula.

 

5. Sadaki: Naira dubu ɗari (₦100,000).

 

6. Jari ga mata: Naira dubu ɗari (₦100,000) domin fara sana’a.

 

Matatar Dangote ta Ƙara Farashin Litar Man Fetur Zuwa Naira 1,275

 

Haka kuma, za a gudanar da gwajin lafiya tare da cike takardun (forms) guda uku domin tabbatar da cewa duk wanda zai shiga shirin ya cika dukkan sharudda, musamman Namiji ya kasance yana da sanaa.

 

A ƙarshe Daurawa ya yi addu’ar Allah ya saka wa gwamna da alkhairi, ya sanya wannan aiki ya zama alheri mai ɗorewa ga al’umma, ya kuma sa ya zama sanadin rage talauci da inganta zaman lafiya a jihar Kano.

 

Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero, ya Gana Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

The post Gwamnatin Kano za ta yi Auren Gata na Mutane Dubu Uku appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow