Gwamnan Yobe ya Zaftare wa Manoma Kashi 50 na Kudin Hayar Taraktocin Noma

Daga Sani Chinade Damaturu.   Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya zaftare wa Manoman jihar kashi 50 cikin 100 na kuɗin hayar Taraktocin Noma.   Sakataren gwamnatin jihar na riko, Dakta Muhammad Goje, ne ya sanar da hakan inda ya baiyana shirin a matsayin wani mataki na rage nauyin da ke kan manoma, fadada damar […] The post Gwamnan Yobe ya Zaftare wa Manoma Kashi 50 na Kudin Hayar Taraktocin Noma appeared first on GTR .

Gwamnan Yobe ya Zaftare wa Manoma Kashi 50 na Kudin Hayar Taraktocin Noma

Daga Sani Chinade Damaturu.

 

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya zaftare wa Manoman jihar kashi 50 cikin 100 na kuɗin hayar Taraktocin Noma.

 

Sakataren gwamnatin jihar na riko, Dakta Muhammad Goje, ne ya sanar da hakan inda ya baiyana shirin a matsayin wani mataki na rage nauyin da ke kan manoma, fadada damar yin noma ta hanyar injinan, habbaka yawan amfanin gona da kuma inganta tattalin arzikin al’ummomin jihar da akasarin su manoma ne.

 

PDP: Babban Malamin Addinin Musulunci, Dakta Abdulkadir Isawa, ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Kujerar Sanatan Bauchi ta Arewa

 

A cewarsa, “Manoma a fadin jihar Yobe sun sami babban ci-gaba a yayin da gwamna Mai Mala Buni, ya amince da rage kashi 50 cikin 100 na kudin hayar motocin noma (Tractors), wanda ya rage kudin daga naira 100,000 zuwa naira 50,000”.

 

A ƙarshe ya jaddada cewa gwamnatinsu za ta ci-gaba da sanya noma a sahun gaba a ajandar ci-gabanta ta hanyar zuba jari mai dorewa a fannin kayan aikin noman kamar Motoci, Injinan noma, ingantattun iri, taki, tallafin noman rani, da sauran shirye-shiryen da suka dace da manoma wadanda aka tsara don ƙarfafa al’ummomin karkara da kuma karfafa tattalin arzikin jihar.

 

Wani Jami’in Tsaro ya Kashe Sama Milyan 1.5 Wajen Bawa Marayu 140 Tallafin Kayan Sallah a Yobe

The post Gwamnan Yobe ya Zaftare wa Manoma Kashi 50 na Kudin Hayar Taraktocin Noma appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow