Gwamnan Bauchi ya Gargadi Sarakunan Jihar Kan Siyar da Filayen Gwamnati ko na Al’umma

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya gargaɗi Sarakunan jihar da su guji siyar da filayen gwamnati ko na al’ummarsu.   Bala Mohammed, ya yi gargaɗin ne a yayin bikin nadin Hakimin Gajin Duguri da kuma Dagatansa guda 36, da Sarkin Duguri, yayi a ranar Asabar a fadarsa da ke […] The post Gwamnan Bauchi ya Gargadi Sarakunan Jihar Kan Siyar da Filayen Gwamnati ko na Al’umma appeared first on GTR .

Gwamnan Bauchi ya Gargadi Sarakunan Jihar Kan Siyar da Filayen Gwamnati ko na Al’umma












Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya gargaɗi Sarakunan jihar da su guji siyar da filayen gwamnati ko na al’ummarsu.

 

Bala Mohammed, ya yi gargaɗin ne a yayin bikin nadin Hakimin Gajin Duguri da kuma Dagatansa guda 36, da Sarkin Duguri, yayi a ranar Asabar a fadarsa da ke garin Duguri na ƙaramar hukumar Alkaleri.

 

Ƙungiyar Kautal Pulaaku Fulbe ta Bukaci Gwamnatin Bauchi ta Gaggauta Share Gonakin da Suka Toshe Hanyoyin Kiwon Dabbobi

 

Gwamnan, wanda Kwamishinan Al’adu da yawon bude ido na jihar Bauchi, Alhaji Abdu Hassan, ya wakilta ya kara da cewa lallai Sarakunan su sa ido kan filayen Masarautunsu tare da nisantar siyar da filayen gwamnati ko na al’umma.

 

Ya kuma bukaci wadanda aka nada Sarautun da su yi hakurin zama lafiya da talakawansu, domin ci-gaban yankin da kasa baki daya.

 

Mun Gamsu da Kamun Ludayin Shugaba Tinubu – Masu Ruwa da Tsakin APC na Jihar Kano

 

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed, ya ce ya nada Alhaji Usman Mohammed, a matsayin Hakimin Gajin Duguri, tare da Dagatai 36 ne domin bunƙasa matsayin gidajen Sarauta a jihar Bauchi.

 

A karshe Sarkin ya gargaɗi Hakimin da Dagatan nasa da su kare Rawunan nasu ta hanyar kamanta gaskiya da hali na gari, tare da sa ido wajen ganin an inganta tsaron yankin ta hanyar nisantar Bata-gari.

 

Hukuncin Kotu Bai Shafi Ƴan Takarar da Muka Tsayar ba — ADC

The post Gwamnan Bauchi ya Gargadi Sarakunan Jihar Kan Siyar da Filayen Gwamnati ko na Al’umma appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow