Duk Al’ummar da ta Fifita Kudi Akan Mutunci, Toh ta Kauce Hanyar Gaskiya – Ambasada Gashash

Daga Bashir Gasau.   Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar Accord a kakar zaben shekarar 2027, Ambasada Dakta Mukhtar Gashash, ya ce duk al’ummar da tafi daraja Dukiya akan mutunci, tabbas ta kauce daga hanyar gaskiya.   Ambasada Gashash, ya baiyana hakan ne ta cikin wani saƙon rubutu da ya aiko wa GTR Hausa […] The post Duk Al’ummar da ta Fifita Kudi Akan Mutunci, Toh ta Kauce Hanyar Gaskiya – Ambasada Gashash appeared first on GTR .

Duk Al’ummar da ta Fifita Kudi Akan Mutunci, Toh ta Kauce Hanyar Gaskiya – Ambasada Gashash












Daga Bashir Gasau.

 

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar Accord a kakar zaben shekarar 2027, Ambasada Dakta Mukhtar Gashash, ya ce duk al’ummar da tafi daraja Dukiya akan mutunci, tabbas ta kauce daga hanyar gaskiya.

 

Ambasada Gashash, ya baiyana hakan ne ta cikin wani saƙon rubutu da ya aiko wa GTR Hausa a daren jiya Asabar, inda rubutun nasa ya kasance kamar haka;

 

“IDAN AL’UMMA TA FI BA DUKIYA DARAJA FIYE DA MUTUNCI, TO TA KAUCE DAGA HANYAR GASKIYA.

 

A da iyayenmu suna koya mana cewa, “Suna mai kyau ya fi dukiya.” Sun gina rayuwarmu ne bisa gaskiya, riƙon amana, mutunci, kunya da aiki tuƙuru. Mutumin kirki shi ne abin koyi, ba wai mai kuɗi kawai ba.

 

Lauya ya Buƙaci Shugaban Ƙaramar Hukumar Nassarawa ya Bashi Cikakken Bayanin Yadda ya Kashe Kudin Al’umma a Shekaru 2

 

Amma yau abin takaici ne. Ba ma tambayar, “Shin mutumin nan mai gaskiya ne? Mai amana ne? Mai tsoron ALLAH ne?” Abin da ake tambaya kawai shi ne, “Nawa yake da shi?”

 

Muna yabon masu Kudi ba tare da tambayar yadda suka samu dukiyarsu ba. Muna girmama masu kuɗi ko da kuwa dukiyarsu ta fito ne daga zalunci, cin hanci, sata ko yaudara. A gefe guda kuma, mutumin kirki mai neman halal da gumin goshinsa ana wulaƙanta shi saboda bai da kuɗi.

 

Malamin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen tarbiyyar al’umma ba a cika darajanta shi ba. Manomin da ke ciyar da ƙasa ana kallonsa da ƙaskantacce. Ma’aikacin da ya ƙi cin hanci ana masa kallon mara wayo. Amma wanda ya tara dukiya ta haramtacciyar hanya shi ake ɗaukaka, a kira shi babban mutum.

 

Satar Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Zamfara ba Abin Mamaki Bane – Rundunar Adalci

 

Wane darasi muke koya wa ‘ya’yanmu?

 

Shin muna koya musu cewa gaskiya ba ta da amfani?

Shin muna koya musu cewa riƙon amana ba ya kawo ci gaba?

Shin muna koya musu cewa kuɗi ne kawai ma’aunin darajar mutum?

 

Idan muka ci gaba da haka, za mu gina al’umma mai cike da arziki amma babu mutunci; mai cike da gidaje na alfarma amma babu zaman lafiya; mai cike da masu mulki amma babu adalci.

 

Babu wata al’umma da za ta ci gaba idan ta rasa mutunci. Babu wata ƙasa da za ta sami zaman lafiya idan gaskiya da riƙon amana suka gushe.

 

A. A. Rano ya Tallafawa Zawiyyar Sheikh Suleiman Geidam da Tirela Biyu ta Siminti Domin Ci-gaba da Aikin Ginin Masallaci

 

Mu koma ga kyawawan dabi’un da kakanninmu suka gada mana: gaskiya, riƙon amana, kunya, tausayi, adalci da aiki tuƙuru. Mu riƙa girmama mutumin kirki ko da bai da dukiya, domin halaye nagari su ne ginshiƙin kowace al’umma mai ɗorewa.

 

Dukiya na iya ƙarewa, amma mutunci yana rayuwa har bayan mutuwar mutum. Suna nagari shi ne mafi girman gadon da mutum zai bari.

 

ALLAH Ya dawo mana da ƙimar gaskiya, Ya ba shugabanninmu hikima, Ya kuma albarkaci ƙasarmu da shugabanni masu tsoron ALLAH da riƙon amana.

 

Mutunci ya fi dukiya. Gaskiya ta fi Kudi. Halaye nagari su ne ginshiƙin ci gaban al’umma.

 

Amb. Dr. Mukhtar Gashash

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano

Accord Party 2027″.

 

 

Hotuna: AIG Garba Ahmed ya Halarci Bikin Yaye Ɗaliban Makarantar Sakandiren ‘Yan Sanda ta Dawakin Kudu da ke Kano

The post Duk Al’ummar da ta Fifita Kudi Akan Mutunci, Toh ta Kauce Hanyar Gaskiya – Ambasada Gashash appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow