Dokar Wa’azi Wajibi ce a Najeriya – Nasiru Salisu Zango

Daga Bashir Gasau.   Fitaccen dan Jaridar nan a Najeriya, Nasiru Salisu Zango, ya baiyana cewa dokar Wa’azi wajibi ce a ƙasar.   Zango ya baiyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda rubutun ya kasance kamar haka;   “Dokar wa’azi wajibi ce a Nigeria   Na dade […] The post Dokar Wa’azi Wajibi ce a Najeriya – Nasiru Salisu Zango appeared first on GTR .

Dokar Wa’azi Wajibi ce a Najeriya – Nasiru Salisu Zango












Daga Bashir Gasau.

 

Fitaccen dan Jaridar nan a Najeriya, Nasiru Salisu Zango, ya baiyana cewa dokar Wa’azi wajibi ce a ƙasar.

 

Zango ya baiyana hakan ne ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda rubutun ya kasance kamar haka;

 

“Dokar wa’azi wajibi ce a Nigeria

 

Na dade Ina neman shugaban da Zai tsaya tsayin daka wajen tabbatar da dokar wa’azi a Arewacin Nigeria.

 

Babban misali ne abin da ya faru ga wannan Malami a cikin masallaci a Sokoto inda Wani matashi ya afka masa shikuma matashin, mabiyan malam suka hallaka shi nan take.

 

Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara ta Tabbatar da Sace Wasu Limamai Bayan Sun Dawo Daga Wajen Taron yi wa Najeriya Addu’a

 

Anan abubuwa uku sun faru, Na farko malam yayi karatu wanda a gun mabiya da yawa, cin fuska ne ga Ma’aiki SAW, abu na biyu, Wani wanda bai ji dadin wa’azin ba yayi yunkurin daukar doka a hannun sa har takai yayi wa Malam rauni abu na uku mafi muni shine, mabiyan Malam sun dauki doka a hannun su sun hallaka wannan matashi.

 

Dokar Wa'azi Wajibi ce a Najeriya - Nasiru Salisu Zango

 

Kenan an bata uku daya bata gyaru ba.

 

Koda akwai a rubuce cikin litattafai dole mutane suji zafi a ransu Idan ana ta maimaita batun matsayin da ake kai iyayen Annabi SAW, shin Wai wanne darasi ake so a koya mana ? Ni fa Ina ganin ko ni da ban Isa komai ba, bazan aminta da duk wani me da’awar yana kaunata ba, amma kuma yayi ta maimaita cewar iyaye na suna wuta, koda ma Suna wutan balle zababbe daga cikin mu mafi madaukakiyar daraja, shin idan ma wannan karatu ya tabbata wacce fa’ida Za’a samu wajen nanata shi?

 

WOFAN da Al’ummar Bagauda Sun Ƙaddamar da Sabuwar Makarantar Firamaren da Suka Gina ta Hanyar Tsarin Ajiyar Kuɗin na Al’umma

 

Shin masu wannan da’awar su ina nasu iyayen suke Kuma Dan Allah ya ya zasu ji Idan aka yi ta maimaita cewar iyayen su Na wutar jahannama?

 

A fahimtata Malam bai kyauta ba Kuma ya kamata wannan abin da ya faru ya zame masa darasi wajen sauya salon karatu, shima marigayi bai kyauta ba domin musulunci bai yadda da daukar doka a hannu ba, kamar yadda almajiran Malam suka fi kowa laifi wajen hallaka musulmi ba tare da bin ka’ida ba.( Wa man qatala mu’uminan…)

 

Anan nake ganin ya kamata gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da bincike a kamo wadanda suka yi kisan domin yin adalci, kana Kuma a tabbatar an yi dokar wa’azi wacce zata ringa sanya kaidi wajen abin da ya dace a karantar.

 

Halayen ‘Yan Najeriya Biyar ne ya Haddasa Musu Fadawa Mawuyacin Halin da Suke Ciki – Abdulkarimu Daiyabu

 

Haka Kuma ya kamata dukkan jihohin Arewacin Nigeria su dabbaka dokar wa’azi domin kiyaye faruwar irin wannan a yankunan su.

 

Musulunci kullum Zaman lafiya yake koyarwa da Kuma kaucewa tsokana, a Nigeria kowa na da ikon yin ibadar sa daidai da fahimtar sa, Mu kiyayi zagi da sukar fahimtar wasu domin suma su kiyayi sukar tamu fahimtar idan muka kiyayi hakan sai Allah ya kiyaye mu. Allah ya hada Kan mu ya magance mana matsalolin saurin kashe mutane da sunan addini”.

 

NASSI ta Shirya Gagarumin Taro Don Bunkasa Kasuwanci a Jihar Kano

The post Dokar Wa’azi Wajibi ce a Najeriya – Nasiru Salisu Zango appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow