Dakta Hayatu ya Tabbatar da Sahihancin Karatun Phd na Dakta Yakubu Adamu a Jami’ar Bamenda ta Kamaru

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.   Ganin yadda siyasar adawa a jihar Bauchi ta shiga lamarin Dr. Yakubu Adamu Dan takarar gwamna a jihar Bauchi na jamiyyar APM, har ya kai ga shiga kafafun labarai ana korafin rashin sahihancin takardar PhD digirin digirgir wanda Dr Yakubu Adamu ya samu daga jamiar Kasa da Kasa ta international […] The post Dakta Hayatu ya Tabbatar da Sahihancin Karatun Phd na Dakta Yakubu Adamu a Jami’ar Bamenda ta Kamaru appeared first on GTR .

Dakta Hayatu ya Tabbatar da Sahihancin Karatun Phd na Dakta Yakubu Adamu a Jami’ar Bamenda ta Kamaru

Daga Mu’azu Hardawa Bauchi.

 

Ganin yadda siyasar adawa a jihar Bauchi ta shiga lamarin Dr. Yakubu Adamu Dan takarar gwamna a jihar Bauchi na jamiyyar APM, har ya kai ga shiga kafafun labarai ana korafin rashin sahihancin takardar PhD digirin digirgir wanda Dr Yakubu Adamu ya samu daga jamiar Kasa da Kasa ta international University of Bamenda da ke kasar kamaru.

 

Batun ya tayar da kura har zuwa yadda wasu kafafun labarai suka yi ta yayata labarun wanda jaridar yanar gizo ta Wikki Times ta fara wallafawa a shafin ta.

 

A saboda haka wakilinmu a Bauchi ya nemi daya daga cikin tsoffin daliban jamiar ta Bamenda Dr Hayatu Mustapha Mohammed Barden Kudun Bauchi Wanda ke aiki a hukumar Pensho ta jihar Bauchi, yadda suka yi doguwar tattaunawa kan wannan batu.

 

Tsohon Grand Khadi na Bauchi ya Buƙaci Gwamnati ta Bawa Mawallafa Littattafai Goyon Baya

 

Cikin jawabinsa Dr. Hayatu ya kawo mana takardun da Tetfund a Nigeria suka yi muamalar karatu da jamiar Bamenda a Kamaru da kuma yadda ma’aikatar ilmi ta gwamnatin tarayyar Nigeria ta gudanar da wasu ayyuka da IUB.

 

Bayan haka Dr Hayatu Mustapha ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda shima tsohon dalibin jamiar ne da ya karanta PhD. a jami’ar, don haka ba za su bari a musu wasa a bata sunan jamiar ba saboda hassadar siyasa.

 

Kuma sanin kowane a shekarun baya dan jihar Bauchi ne shugaban kungiyar tsoffin daliban jamiar ta Bamenda a Nigeria.

 

Matsalolin Almajirci a Najeriya: Gwamnatin Tarayya ta yi Iya Nata, Saura Jihohi da Ƙananan Hukumomi – Dakta Balarabe Kakale

 

Don haka sun sha yin taron tsoffin daliban jamiar ta Bamenda a Bauchi. Kasancewar shugaban kungiyar ya sauka an zabi sabo daga wata jihar shi yasa yanzu taron ya koma wata jihar.

 

Dr Hayatu Mustapha ya bayyana cewa akwai Profesa Ambiza da Profesa Cletus Wanda sune suka fara duba rubuce rubuce da nazarin da Dr Yakubu Adamu ya yi na kwanaki 150 sai prof Ambiza ya rasu. Kuma da wannan nazarin ayyukan sa na PhD suka kammala.

 

Daga nan sai aka hada Shi da Alhaji Kawu Gana Bursar na Federal polytechnic Bauchi wanda shima tsohon dalibin jami’ar Bamenda ne, shine ya kammala tattara ayyukan ya gabatar da su wa jamiar ta Bamenda kamar yadda aka tsara.

 

Ku Dauki Mataki Kafin Hakurin Musulmin Najeriya ya Kare – Sakon NSCIA ga Gwamnatin Tarayya

 

Kuma a halin yanzu Dr Kawugana yana koyarwar wucin gadi a federal poly da Open University da wasu cibiyoyin ilmi.

 

Kuma saboda kwarewarsa a fannin kudi da aikin banki, hukumar bada tallafin kudin karo ilmi ta Kasa Tetfund ta amince da wasu manyan littafai kusan goma da ya rubuta Tetfund suka dauki nauyin bugawa don rabawa daliban Nigeria a manyan makarantu don ci gaban ilmi, duk ya nuna su ga wakilin mu.

 

Harwa yau Alhaji Kawu Gana ya halarci tarukan bita da karawa juna sani a ciki da wajen Nigeria yadda suma ya nuna kadan daga cikin takardun shaidar sama da guda 20 ga wakilin mu.

 

Manhajar WhatsApp ya Fara Ƙaddamar da Sabon Tsarin Yin Rijista ba Tare da Lambar Waya ba

 

Don haka Dr Hayatu Mustapha Barden Kudun Bauchi ya kara da cewa maganar takardar PhD ta Dr. Yakubu Adamu akwai matsala sharrin siyasa ce da hassada komai nasa game da takardun nazarin PhD yana da ingattacciyar madogara daga wannan jamiar ta Bamenda.

 

Don haka nan gaba za mu sake neman wasu tsoffin daliban da shi kan sa Dr Yakubu Adamu za mu tattauna da su don sake samun karin bayani kan batun.

 

Da fata jama’a za su kauce wa cin mutuncin juna game da danganta siyasa da hanyoyin cin zarafin mutane don a mutunta aiki da karatun kowane mai sha’awar siyasa don a dama da shi kamar yadda kundin tsarin Mulki ya ba kowa damar shiga siyasa a Najeriya.

 

Hotuna: Yadda Sarkin Hadejia ya Karbi Bakuncin Matar Shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu

The post Dakta Hayatu ya Tabbatar da Sahihancin Karatun Phd na Dakta Yakubu Adamu a Jami’ar Bamenda ta Kamaru appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow