CPFA-MN ta Shirya Bita ta Shekara-shekara Kan Sha’anin Tsaro a Najeriya

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Ƙungiyar bada agajin gaggawa da samar da tsaro a Najeriya, wato Citizen for Peace and First Aid Mission of Nigeria (CPFA-MN), ta shirya bita ta shekara-shekara akan sha’anin tsaro a ƙasar.   Col. I.I Amara me ritaya, shine Kwamanda Janar na rundunar, ya ce taron na bana ya sami halartar […] The post CPFA-MN ta Shirya Bita ta Shekara-shekara Kan Sha’anin Tsaro a Najeriya appeared first on GTR .

CPFA-MN ta Shirya Bita ta Shekara-shekara Kan Sha’anin Tsaro a Najeriya

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Ƙungiyar bada agajin gaggawa da samar da tsaro a Najeriya, wato Citizen for Peace and First Aid Mission of Nigeria (CPFA-MN), ta shirya bita ta shekara-shekara akan sha’anin tsaro a ƙasar.

 

Col. I.I Amara me ritaya, shine Kwamanda Janar na rundunar, ya ce taron na bana ya sami halartar manyan hukumomin tsaro, domin ƙarfafa musu guiwa wajen gudanar da aiyukansu.

 

Hotunan ‘Yan Jaridu Biyar da Gwamnatin Nijar ke Tsare da su a Gidan Yari

 

A cewar Amara, ” Muna da kyakkyawar alaka a tsakaninmu da dukkan hukumomin tsaron Najeriya, adan haka suka amince su zo su bawa mambobinmu bita domin su kara samun kwarewa a aiyukansu na yau da kullum”.

 

A nasa ɓangaren Kwamandan rundunar na Abuja, Abdulrazak Adenomo, ya ce tsaro lamari ne da ya shafi dukkan al’umma ba wai daidaikun mutane ba, saboda haka akwai bukatar haɗin-kai a tsakanin mahukuntan da al’ummar gari wajen magance dukkan matsalolin tsaro.

 

Babu Mai Hankalin da Zai Zaɓi Tinubu a Arewacin Najeriya – Dakta Sunusi Balarabe na Jam’iyyar APC

 

Daga bisani Kakakin Kungiyar na Kasa, Ambasada Sulaiman Abdulrashid, ya ce manufar rundunar tasu shine taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro, da kuma bada dukkan wani agajin gaggawa a lokacin da wani Iftila’i ya faru.

 

Kalaman Ministan Shari’a Akan ADC Wauta da Rashin Hankali ne – Honarabul Shu’aibu Miƙati

 

A ƙarshe mahalarta taron sun bada tabbacin yin amfani da ilimin da suka koya, ta yadda za su bada tasu gudunmawar ta fuskar bada agajin gaggawa da kuma samar da tsaron a lungu da saƙo na Najeriya.

 

Taken taron na bana shine “Rashin Tsaro na Ƙasa da Gina Juriya ta Ƙasa: Alaƙar Tsaron Ƙasa”, inda za a kammala a yau Lahadi bayan shafe kwanaki hudu ana gudanarwa.

 

Dakta Yahuza Getso ya Zama Garkuwan Tsaron Arewa

The post CPFA-MN ta Shirya Bita ta Shekara-shekara Kan Sha’anin Tsaro a Najeriya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow