Atiku ya Kai Tinubu Ƙara Kotu Kan Cancantarsa ta Tsayawa Takarar Zaɓen 2027

Daga Bashir Gasau.   A jiya Jumu’a ne Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana ƙalubalantar cancantar Shugaba, Bola Ahmed Tinubu, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, bisa zargin jabun takardar shaidar yi wa kasa hiidma (NYSC Certificate).   Ku Guji […] The post Atiku ya Kai Tinubu Ƙara Kotu Kan Cancantarsa ta Tsayawa Takarar Zaɓen 2027 appeared first on GTR .

Atiku ya Kai Tinubu Ƙara Kotu Kan Cancantarsa ta Tsayawa Takarar Zaɓen 2027


















Daga Bashir Gasau.

 

A jiya Jumu’a ne Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yana ƙalubalantar cancantar Shugaba, Bola Ahmed Tinubu, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, bisa zargin jabun takardar shaidar yi wa kasa hiidma (NYSC Certificate).

 

Ku Guji Aikata Abubuwa Marasa Kyau a Ranar Takutaha – Malam Ibrahim Mai Ashafa

 

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya je Kotun da kansa domin rantsar da takardar shaidar da ke goyon bayan ƙarar, wadda suke karar Shugaba Tinubu, Jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe (INEC).

 

Ƙarar ta dogara ne kan Sashe na 137(1)(j), 139(1)(a)(i), da 285(14)(c) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da kuma wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.

 

NAHCON ta Sanar da Kuɗin Aikin Hajjin Shekarar 2027

 

Babban abin da ake magana a kai shi ne Sashe na 137(1)(j), wanda ya hana duk wanda ya gabatar wa INEC da takardar shaidar bogi tsayawa takarar Shugaban Ƙasa, tare da neman INEC ta gabatar da Form CF001 na Tinubu da aka gabatar a zaɓen 2023 da kuma na 2027.

 

Masu ƙarar na neman kotu ta yanke hukunci kan ko ya kamata a hana Tinubu da APC shiga zaɓen 2027, bisa zargin cewa Shugaban ya gabatar wa INEC da takardar shaidar kammala NYSC mai ɗauke da sunan “Tinubu Bola Adekunle” a zaɓen 2023 da kuma na 2027.

 

Ku Tabbatar an Gudanar da Sahihin Zaɓe a Jihar Osun – Umarnin Tinubu ga INEC da Hukumomin Tsaro

The post Atiku ya Kai Tinubu Ƙara Kotu Kan Cancantarsa ta Tsayawa Takarar Zaɓen 2027 appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow