Al’ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya

Daga Bashir Gasau.   Al’ummar garin Alhaji Tagidadu dake mazabar Rantan a Karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano, sun koka kan halin kunchin da suke ciki a sakamakon halin ko in kula da Mahukunta suka yi da su.   Garin ne mai adadin mutane kimanin 3,000, wadanda suke a dunkule guri guda ba kamar yadda […] The post Al’ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya appeared first on GTR .

Al’ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya












Daga Bashir Gasau.

 

Al’ummar garin Alhaji Tagidadu dake mazabar Rantan a Karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano, sun koka kan halin kunchin da suke ciki a sakamakon halin ko in kula da Mahukunta suka yi da su.

 

Garin ne mai adadin mutane kimanin 3,000, wadanda suke a dunkule guri guda ba kamar yadda aka saba ganin mafiya yawancin kauyuka ba, sun ce duk wasu kayan more rayuwar da ake samu albarkacin romon Demokradiyya da ake kafafa dashi basu san ana yi ba.

 

Akwai Buƙatar Masu Ruwa da Tsakin Jihar Bauchi su Gaggauta Ceto Ginin Tarihi na Baban Gwani Gidan Madaki

 

Da yake yi wa GTR Hausa karin haske, shugaban kungiyar matasan garin, Sale Jibrin Tagidadu, ya ce duk da garin nasu babba ne amma hanyar shiga ta lalace la’akari da yadda tun lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Bebeji na lokacin, Dankaka Hussaini Bebeji, yayi musu hanyar wadda yanzu ta lalace amma mahukunta sunyi buris da su.

 

Al'ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya

 

A cewarsa, “Makaranta kwaya daya tilo muke da ita tun kusan shekaru 20 da gina ta, kuma yanzu ta mutu babu koda fallen rufin kwano guda daya, gininta ma ya rurrushe, yaranmu sama da dari 3 da suke zuwa makarantar yanzu sam basa zuwa”.

 

Hotuna: Yadda Fursunoni 52 ke Zana Jarrabawar NECO/NABAIS a Gidajen Gyaran Hali na Kano

 

Musa Jibrin Tagidadu da ke a matsayin daya daga cikin Malaman Makarantar, ya ce tun sama da shekaru 4, gindin bishiyu ya zama wajen da Malaman makarantar ke bawa Dalibai darasi.

 

Al'ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya

 

Shima daya daga cikin Dattawan yankin, Ahmadu na Mata Mai Unguwa, ya ce basu da ruwan sha ballantana na wanka, kuma duk yawan nan nasu duk musulmai ne, amma babu masallacin Jumu’a, dole sai sun tsallake kogi tare da yin doguwar tafiya zuwa garin Rantan ko Tiga sannan su yi sallar Jumu’a, wanda duk lokacin da aka ce ruwa ya kawo a wannan kogi suna ji suna gani sallar Jumu’a ke gagarar su”.

 

UCA ta Yabawa Gwamnatin Najeriya Bisa Tantancewa Tare da Amincewa da Sahihancin Wasu Jami’oin Nijar

 

Adan haka suke rokon Mahukunta da sauran al’umma da su kawo musu dauki, ta yadda za su sami damar yin addini cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

 

A karshe al’ummar garin sun sha alwashin kauracewa rumfunan zabe a shekarar 2027, tunda sun shafe tsawon shekaru sun zaben amma kwalliya taki biyan musu kudin Sabulu.

 

Asiri ya Kuma Tonuwa Kan Kafa Hukumar Bogi a Najeriya

The post Al’ummar Garin Alhaji Tagidadu Sun yi Barazanar Kauracewa Zaben 2027 Saboda Rashin Sharbar Romon Demokradiyya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow