Akwai Buƙatar Shugaba Tinubu ya Waiwayi Ƙudirin Tabbatar da Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya – Godwin Ayinda

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Shugaban Kungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya reshen jihar Nasarawa (VGN), Godwin Jeyi Ayinda, ya buƙaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya waiwayi ƙudirin dokar tabbatar da Kungiyar a hukumance.   Godwin Ayinda, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa a Abuja, inda a lokacin da yake baiyana […] The post Akwai Buƙatar Shugaba Tinubu ya Waiwayi Ƙudirin Tabbatar da Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya – Godwin Ayinda appeared first on GTR .

Akwai Buƙatar Shugaba Tinubu ya Waiwayi Ƙudirin Tabbatar da Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya – Godwin Ayinda

Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Shugaban Kungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya reshen jihar Nasarawa (VGN), Godwin Jeyi Ayinda, ya buƙaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya waiwayi ƙudirin dokar tabbatar da Kungiyar a hukumance.

 

Godwin Ayinda, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa a Abuja, inda a lokacin da yake baiyana shirin da suka yi a lokacin bikin babbar Sallah.

 

Mafi Alherin Rana Itace Ranar Arafah, Saboda Haka Ku Yawaita Addu’oi – Farfesa Isah Pantami

 

A cewarsa, “Ina tunasar da gwamnatin tarayyar Najeriya, ƙarkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, da ta waiwayi ƙudirin dokar da ke neman tabbatar da kungiyar ‘yan sintiri domin ta shiga cikin jerin hukumomin tsaron ƙasar nan”.

 

Dadin dadawa ya sha alwashin cewa, jami’ansu za su yi aiki tukuru ta hanyar kara kaimi, wajen ganin an gudanar da Sallar Idin da kuma sauran shagulgulan Sallah cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali.

 

Ku Daina Yaudarar Talaka ta Hanyar Bashi Babur, Mota ko Fili – Saƙon CHRCDI ga ‘Yan Siyasar Najeriya

 

Ya Kuma yabawa gwamnatin jihar Nasarawa a bisa yadda take sauraron kokensu ba tare da nuna bambancin addini ko yare ba, inda ya kara jaddada aniyar Ƙungiyar na tabbatar da zaman lafiya a ɗaukacin kananun hukumomi jihar guda 13.

 

A ƙarshe rundunar ta ja hankalin al’umma da su kasance masu basu bayanan sirri domin tabbatar da tsaro, musamman a tsakanin mazauna Unguwannin dake faɗin jihar.

 

Gwamnan Kano ya Bada Barka da Sallar Naira Dubu 20 ga Dukkan Ma’aikatan Gwamnatin Jihar

The post Akwai Buƙatar Shugaba Tinubu ya Waiwayi Ƙudirin Tabbatar da Ƙungiyar ‘Yan Sintiri ta Najeriya – Godwin Ayinda appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow