Akwai Buƙatar Musulmi da Kirista su Hada Hannu Wajen Koyar da Ilimin Addinansu a Makarantun Firamare da Sakandiren Arewacin Najeriya – Rabaran Kunama

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Babban Sakatare Kuma Mai bada shawara a Cibiyar bunkasa Ilimin addinin Kirista a Najeriya (CEDAC), Rt. Rabaran Dakta Ishaya Kunama, ya bukaci masu ruwa da tsaki su hada hannu da Cibiyar domin inganta harkokin koyo da koyawar a darussan addinin Kirista dama na Musulunci a makarantun firamare da Sakandiren da […] The post Akwai Buƙatar Musulmi da Kirista su Hada Hannu Wajen Koyar da Ilimin Addinansu a Makarantun Firamare da Sakandiren Arewacin Najeriya – Rabaran Kunama appeared first on GTR .

Akwai Buƙatar Musulmi da Kirista su Hada Hannu Wajen Koyar da Ilimin Addinansu a Makarantun Firamare da Sakandiren Arewacin Najeriya – Rabaran Kunama












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Babban Sakatare Kuma Mai bada shawara a Cibiyar bunkasa Ilimin addinin Kirista a Najeriya (CEDAC), Rt. Rabaran Dakta Ishaya Kunama, ya bukaci masu ruwa da tsaki su hada hannu da Cibiyar domin inganta harkokin koyo da koyawar a darussan addinin Kirista dama na Musulunci a makarantun firamare da Sakandiren da ke Arewacin Najeriya.

 

Abinda ya Kamata Talakawa su Sani Kan Shekarun Najeriya 27 a Tafarkin Demokradiya (2) – Abdulkarimu Daiyabu

 

Ishaya Kunama, ya baiyana hakan ne a yayin zantawarsa da GTR Hausa a Abuja, a lokacin da yake tsokaci dangane da kamun ludayin Sa kan sabon mukamin shugabancin Cibiyar ta CEDAC, da ya rabauta da shi a farkon wannan shekarar ta 2026.

 

A cewarsa, “Tunda na fari aiki a matsayin babban Sakatare na wannan cibiya cikin watan janairun shekarar 2026, na dauki matakan ganin al’umma sun rungumi nazartar ilimin addinin Kirista a kwalejin horas da manyan Malamai dama jami’oin Najeriya domin zama kwararrun Malamai a fannin”.

 

Alhazan Najeriya 35,993 Sun Dawo Gida Daga Ƙasar Saudiyya a Sawu 91

 

Kunama wanda ke a matsayin Bishop dake Kula da aiyuka na musamman a majam’iar Medodist dake yankin Arewacin Najeriya, ya kara da cewa ko gwamnatin jihar Kaduna da ta gabata dama wasu jihohin Najeriya sun yi jarrabawar tantance kwarewar Malamai dake koyar da darussan addinin Kirista dama na Musulunci wato (CRK da IRK) da sauran Malaman makarantun firamare da sakandire, amma an Sami wasu da rashin gogewar da ta dace a ce Malami nada ita, lamarin da ya tilastawa gwamnati sallamarsu daga bakin aiki tare da maye gurbinsu da wadanda suka fisu cancanta.

 

Adon haka ne ya sha alwashin yin aiki da kwarewarsu tare da kira da sauran Masana domin suyi aiki tare da nufin kaiwa ga cikakkiyar nasara.

 

Rahoton Zanga-zangar Alummar Garin Yakasan Ƙarfi Kan Zargin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kura da Gine Musu Hanya

 

Malamin addinin na Kirista ya shawarci gwamnati da ta dauki Malaman wucin gadi domin cike gibin da ake da su, musamman a yankunan karkara da yanzu haka keda karancin Malamai sakamakon rikice-rikicen dake sanya fargaba a zukatan wasu Malamai, da idan an tura su zuwa yankunan karkara da kauyuka suke nukusani saboda barazanar tsaro.

 

An dai kafa cibiyar ta (CEDAC) ne a shekarar 1947, da nufin bada shawara kan bunkasa Ilimin addinin Kirista da Kuma ikilisiyoyi a Arewacin Najeriya.

 

Hotuna: Yadda AUFCDN ta Gudanar da Taronta na Arewa Maso Yamma

 

The post Akwai Buƙatar Musulmi da Kirista su Hada Hannu Wajen Koyar da Ilimin Addinansu a Makarantun Firamare da Sakandiren Arewacin Najeriya – Rabaran Kunama appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow