Zamu Ci-gaba da Bin Hakkinmu Duk da INEC ta Wallafa Sunan Angbozo – Lauyan Abdullahi Muhammad Hassan

Daga Kallamu Galadima Dambo.   Dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a Jam’iyyar ADC, Abdullahi Muhammad Hassan, ya ce zai ci gaba da bin hakkin takararsa duk da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), ta wallafa sunan Nuhu Angbozo.   Lauyan Abdullahi, Barista Muhammad Adamu Wamba, ne ya baiyana wannan matsaya a yayin zantawarsa […] The post Zamu Ci-gaba da Bin Hakkinmu Duk da INEC ta Wallafa Sunan Angbozo – Lauyan Abdullahi Muhammad Hassan appeared first on GTR .

Zamu Ci-gaba da Bin Hakkinmu Duk da INEC ta Wallafa Sunan Angbozo – Lauyan Abdullahi Muhammad Hassan












Daga Kallamu Galadima Dambo.

 

Dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a Jam’iyyar ADC, Abdullahi Muhammad Hassan, ya ce zai ci gaba da bin hakkin takararsa duk da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), ta wallafa sunan Nuhu Angbozo.

 

Lauyan Abdullahi, Barista Muhammad Adamu Wamba, ne ya baiyana wannan matsaya a yayin zantawarsa da GTR Hausa, Jim kadan baya INEC ta wallafa sunan abokin Hamaiyarsa na cikin gida, Manjo Janar Nuhu Angbazo Mai ritaya, inda ya ce guiwarsu ba tayi sanyi ba.

 

Zamu Ci-gaba da Bin Hakkinmu Duk da INEC ta Wallafa Sunan Angbozo - Lauyan Abdullahi Muhammad Hassan

 

Barista Wamba, ya kara da cewa tunda lamarin yana gaban Kotu, toh za su jira ranar 28 ga watan Satumba me kamawa, domin Kotu ta dawo musu da nasarar su tunda su al’ummar jihar Nasarawa suka zaba.

 

A ƙarshe ya buƙaci al’umma da sauran magoya baya su kwantar da hankalinsu su jira hukuncin Kotu, wadda ya ce yana da yakinin za ta tabbatar da adalci ta hanyar bawa me gaskiya nasara.

The post Zamu Ci-gaba da Bin Hakkinmu Duk da INEC ta Wallafa Sunan Angbozo – Lauyan Abdullahi Muhammad Hassan appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow