‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Wasu Tarin Alburusai da Aka Boye a Kusa da Maƙabarta

Daga Aliyu Gerengi Gombe.   Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe, ta sami nasarar gano wasu Alburusai da aka ɓoye a kusa da wata Makabarta.   Kakakin rundunar na jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce an gano Alburusan ne […] The post ‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Wasu Tarin Alburusai da Aka Boye a Kusa da Maƙabarta appeared first on GTR .

‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Wasu Tarin Alburusai da Aka Boye a Kusa da Maƙabarta

Daga Aliyu Gerengi Gombe.

 

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Gombe, ta sami nasarar gano wasu Alburusai da aka ɓoye a kusa da wata Makabarta.

 

Kakakin rundunar na jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa GTR Hausa, inda ya ce an gano Alburusan ne a gefen hanyar Kalshingi, kusa da makabarta a Kwadon ta ƙaramar hukumar Yamaltu Deba.

 

Majalisar Tsaron Jihar Yobe ta Gargadi Al’umma Kan Rikicin Siyasa

 

A cewar Buhari, “Jami’anmu sun gano Alburusai masu rai kirar 7.62mm guda Dari da Goma Sha Tara (119) waɗanda aka ɓoye a cikin buhu, bayan samun sahihan bayanai da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar jiya Talata, kan ganin buhun da aka ɓoye a ƙarƙashin wata bishiya”.

 

Kayan da aka samu a wurin sun ƙunshi Alburusai (119), Buhuna biyu na kwanson Alburusai, Kwalabe biyu masu ɗauke da ƙwayar zogale da kuma Koriyar jaka guda ɗaya.

 

UDUTH ya Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya

 

Haka kuma Jami’an sun gudanar da bincike a cikin dajin da kewayen wurin, amma ba su kama kowa ba, adan haka rundunar ta ƙara tsaurara sa ido da sintiri a yankin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano tare da cafke waɗanda ke da hannu wajen ɓoye harsasan.

 

A ƙarshe Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ya yi kira ga mutane da su ci-gaba da kasancewa cikin shiri, tare da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.

 

Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano

The post ‘Yan Sandan Gombe Sun Gano Wasu Tarin Alburusai da Aka Boye a Kusa da Maƙabarta appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow