UDUTH ta Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya

Daga Dr. Balarabe Shehu Kakale.   Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto (UDUTH), ya sake kafa tarihi bayan samun nasarar gudanar da dashen ƙoda a karo na biyu.   Likitocin Asibitin sun yi wa wata budurwa mai shekaru 22 dashen ƙodar cikin nasara a watan Afrilun shekarar 2026, a cibiyar ƙwararru ta […] The post UDUTH ta Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya appeared first on GTR .

UDUTH ta Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya

Daga Dr. Balarabe Shehu Kakale.

 

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto (UDUTH), ya sake kafa tarihi bayan samun nasarar gudanar da dashen ƙoda a karo na biyu.

 

Likitocin Asibitin sun yi wa wata budurwa mai shekaru 22 dashen ƙodar cikin nasara a watan Afrilun shekarar 2026, a cibiyar ƙwararru ta Centre of Excellence in Urology and Nephrology (CEUN).

 

Rahotanni sun nuna cewa dashen ƙodar na farko da asibitin ya gudanar cikin nasara ya kasance ne a watan Janairun 2025 ga wani namiji mai shekaru 32. Sai dai a wannan karo aikin yafi ɗaukar hankali al’umma saboda yadda ya gudana a ƙarƙashin ƙwararrun likitocin Asibitin, ba tare da dogaro da ƙwararrun ƙasashen waje ba.

 

Kwankwaso na Yiwa Tinubu Aiki ne a Fakaice Don ya Sake Lashe Zaɓen 2027 – Kakakin Gwamnan Kano

 

Tawagar ƙwararrun da suka gudanar da aikin sun haɗar da likitocin cututtukan koda, likitocin tiyata, masana aikin jijiyoyi, likitocin bacci yayin tiyata, masana magunguna, ma’aikatan jinya na musamman, masana binciken ɗakunan gwaje-gwaje da kuma injiniyoyin kayan aikin lafiya.

 

UDUTH ya Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya

 

Masana sun bayyana wannan nasara a matsayin wani babban ci-gaba da zai taimaka wajen rage tsadar neman magani a ƙasashen waje, rage jinkiri wajen samun kulawa, haɓaka bincike da ƙwarewar likitoci, tare da ƙarfafa tsarin kula da lafiya a Najeriya.

 

An danganta wannan ci-gaba da dogon tarihin ilimi da kimiyya, da Daular Sokoto ta assasa tun sama da shekaru 200 da suka gabata.

 

Hotuna: Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta Baiyana Nasarar da ta Samu a Cikin Kwanaki 30

 

Wani fitaccen misali shi ne littafin “Amrilil Kulyati Wa Ilajiha” wanda Sultan Muhammadu Bello ya rubuta tsakanin shekarun 1817 zuwa 1837, littafin da ya mayar da hankali kan cututtukan koda da hanyoyin magance su.

 

UDUTH ya Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya

 

Tarihin ya nuna cewa Sultan Muhammadu Bello ya rubuta maganin ne bayan ya duba wata matsalar rashin lafiya da Sarkin Zazzau, Malam Yamusa, ya kamu da ita, inda daga bisani ya samu cikakkiyar lafiya bayan amfani da maganin da Sultan ɗin ya tsara.

 

Masana tarihi sun baiyana wannan a matsayin ɗaya daga cikin manyan shaidu, da ke nuna irin ci-gaban ilimin lafiya da aka samu a Daular Sokoto tun ƙarni na 19.

 

Na fi Kowa Cancantar Zama Gwamnan Jihar Katsina – Tsohon Shugaban DSS na Najeriya Lawal Daura

 

Masu sharhi sun ce abin alfahari ne yadda jami’ar da aka sanya wa sunan Shehu Usmanu Danfodiyo, ta samar da ƙwararrun likitoci da masana, waɗanda a yanzu suke gudanar da ɗaya daga cikin manyan aiyukan lafiya mafi wahala a duniya wato aikin dashen Ƙoda.

 

Domin tunawa da wannan tarihi, ƙungiyar SokotoDNA ta kai ziyara fadar Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli, inda ta gabatar masa da kwafin littafin Sultan Muhammadu Bello kan cututtukan Ƙoda tare da samfurin tsarin koda ta jikin ɗan Adam domin nuna gudunmawar shugabannin Daular Sokoto a fannin lafiya da kimiyya.

 

Rahoton ya bayyana cewa Sarkin Zazzau na wancan lokaci, Malam Yamusa, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ilimin magungunan gargajiya da na lafiya a masarautar Zazzau, lamarin da ya sanya yankin ya zama cibiyar neman magani tun shekaru Aru-aru.

 

Mun Shirya Yaƙar Maguɗin da Aka yi Mana a Zaben Gwamnan Jihar Kaduna a 2023 – Honarabul Kudan na ADC

 

Marubucin ya jaddada cewa tarihin Daular Sokoto bai tsaya ga yaƙe-yaƙe kawai ba kamar yadda wasu ke ƙoƙarin nunawa, Inda ya ce daular ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa ilimi, zaman lafiya, tattalin arziki, kimiyya, fasaha, magunguna, kare haƙƙin ɗan Adam da kuma ci-gaban rayuwar al’umma.

 

A cewarsa, “Daular Sokoto ta kasance ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi, bincike da cigaban ɗan Adam a ƙarni na 19, inda aka samar da rubuce-rubuce da koyarwa a fannoni daban-daban na rayuwa ciki har da lafiya, addini, shari’a da kuma zamantakewa”.

 

Jirage 94 Sun yi Jigilar Maniyyatan Najeriya 37,393 Zuwa Kasar Saudiyya

 

Ya kuma yabawa shugabannin UDUTH da CEUN tare da dukkan likitocin, ma’aikatan jinya, masana bincike da injiniyoyi bisa wannan babbar nasara da suka samu.

 

Masana da al’umma da dama sun bayyana wannan nasara a matsayin wata alama ta ci-gaban Najeriya a fannin lafiya, tare da nuna cewa idan aka ci gaba da zuba jari a fannin ilimi, binciken ƙwararru, ƙasar nan za ta iya rage dogaro da ƙasashen waje wajen manyan aiyukan lafiya.

 

A ƙarshe sun bayyana nasarar dashen Ƙodar da UDUTH ta samu a matsayin haɗuwar tarihi da ci-gaban zamani, na tsohon gadon ilimi da bincike da Daular Sokoto ke ci-gaba da baiyana, a cikin sababbin nasarorin kimiyya da lafiya a wannan zamani.

 

Mata Masu Rawar Gala Sun Karɓi Addinin Musulunci a Hannun Hukumar Tace Fina-finai ta Kano

The post UDUTH ta Sami Nasarar Yin Dashen Ƙoda Karo na Biyu, Albarkacin Tunawa da Gudunmawar Sultan Muhammadu Bello a Fannin Kiwon Lafiya appeared first on GTR .

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow